An rawaito cewa sojoji sun kama mutum biyu da ake zargi da lalata kayayyaki a garin Otukpo, karamar hukumar Otukpo, jihar Binuwe.
An ce an kama wadanda ake zargin ne yayin da suke lalata kayan aiki da abubuwan more rayuwa a wajen masana’antar Binuwe Burnt Bricks da ke Otukpo.
- Matasa 2 Sun Mutu Bayan Nutsewa A Rafi A Kano
- Dalilin IFAD Na Zuba Naira Biliyan 16 A Fannin Noma A Benuwe
Majiya ta ce wadanda ake zargin sun kai hari kamfanin da ke kan babbar hanyar tarayya a Otukpo a daren Asabar, amma sojoji da ke wurin sun kamo su.
An bayyana sunayen wadanda ake zargin Wilson Egbanga mai shekara (16) da Okoh Akoja mai shekara (40), wadanda dukkaninsu suka ce mazauna Karamar Hukumar Otukpo ne.
Wani mazaunin Otukpo, da aka ambaci sunansa Adaji, ya shaida wa wakilinmu cewa wasu mutane da ke wurin da suka ga wadanda ake zargin sun kai rahoto ga sojoji, wadanda suka dauki mataki nan take, wanda ya kai ga kama su.
Shugaban Karamar Hukumar Otukpo, Madwell Ogiri, ya tabbatar da kama wadanda ake zargin lalata kayayyaki, inda ya ce an mika su ga jami’an Hukumar Tsaro ta Jiha (DSS) a Otukpo.
Shugaban, wanda ya yi magana ta hanyar mai ba shi labarai, Joshua Otene, ya ce: “An kama wadanda ake zargin a wurin aikinsu,” sannan ya jera kayan da aka samu a hannunsu, ciki har da karafa da yawa, bututun gas biyu masu girma, da karamin bututun gas din da aka hada da hoses da ake zargin an yi amfani da su wajen yanka karfe.
Ya kara da cewa, “A yayin tambayoyin farko, wadanda ake zargin sun ce an ja hankalinsu zuwa aikata laifin ne ta hannun wani mutum mai suna Omagbo, wanda ake cewa yana tukin motar Hi-Jet fara a cikin al’ummomin da ke iyaka da wajen Binuwe Burnt Bricks.
“Amma shugaban kungiyar da ake zargin, har yanzu yana bacewa.”
Lokacin da aka tuntubi mataimakin kwamandan DSS na Otukpo, Mr Aba Bashi, ta wayar tarho, ya tabbatar da kama wadanda ake zargin sannan ya ce har yanzu suna hannunsu kuma za a mika su zuwa Makurdi nan ba da jimawa ba.
“Gaskiya ne cewa sojoji sun kawo mutane biyu da ake zargin lalata kayayyaki zuwa ofishinmu. Za a mika su zuwa Makurdi nan ba da jimawa ba,” in ji Bashi.
Lalacewar kayayyakin more rayuwa na daga cikin manyan barazanar da ke kalubalantar ci gaban Nijeriya da harkokin masana’antu, inda yake lalata dukiyar jama’a kuma yana kawo cikas ga kokarin bunkasa kasa.
Binuwe Burnt Bricks an kafa shi ne a zamanin marigayi Gwamna Aper Aku, amma ya kasance a kashe shekaru da dama, inda wasu kayan aiki da abubuwan more rayuwa suka lalace.
Kokarin samun martanin Kwamandan ‘Yansanda na Jihar bai samu nasara ba, domin kakakin rundunar, DSP Udeme Edet, bai amsa kiran waya ko sakonnin waya da aka tura mata zuwa wayarta ba har lokacin kammala wannan rahoto.