Sojojin Runduna ta 3 ta Sojojin Nijeriya tare da Operation SAFE HAVEN (OPSH) sun ceto fasinjoji 16 da aka yi garkuwa da su a kan hanyar Jos-Mangu a Jihar Filato.
A cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na OPSH, Major Samson Zhakom, ya fitar a Jos, an bayyana cewa aikin ceto ya fara ne lokacin da Sojoji da ke gudanar da aikin Operation LAFIYAR JAMA’A suka gano mota ba kowa a ciki a gefen hanya a Mararraban Kantoma cikin ƙaramar hukumar Mangu. Sojojin sun bincika daji kusa da motar don gano mutanen da ake zargin an yi garkuwa da su.
Sanarwar ta kara da cewa, lokacin da ‘yan fashin suka ga sojojin, sun buɗe musu wuta sosai sai hakan ya sa ‘yan fashin suka gudu tare da barin fasinjojin..
- Adadin Waɗanda Suka Mutu A Sabon Harin ‘Yan Bindiga A Filato Ya Kai 52
- Mutum 45 Sun Rasa Rayukansu A Wani Sabon Hari A Filato
Sojojin sun gudanar da bincike a yankin gaba ɗaya, inda suka ceto dukkanin fasinjojin 16, ciki har da yara guda shida. An kuma ba wa wasu daga cikin waɗanda aka ceto taimakon farko, bayan sun ji raunuka kaɗan a lokacin lamarin.
A ƙarshe, OPSH ta tabbatar da cewa Sojojin sun raka fasinjojin zuwa wajen lafiya don ci gaba da tafiyarsu zuwa birnin Jos. Hakanan, Sojojin OPSH suna ci gaba da neman ‘yan fashin da suka tsere, waɗanda ake zaton sun ji raunuka a yayin harbin da ya faru.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp