Dakarun sojin Nijeriya sun ceto wasu mutane shida da aka yi garkuwa da su a wani sintiri na share fage da suka gudanar a kewayen yankin Kangon Kadi a karamar hukumar Chikun a Jihar Kaduna.
Kwamishinan tsaron cikin gida na jihar, Samuel Aruwan ne, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin a Kaduna.
- Adadin Wadanda Suka Mutu Sakamakon Girgizar Kasa Mai Karfin Maki 6.8 Da Ta Afku A Lardin Sichuan Ya Kai 93
- An Kaddamar Da Yarjejeniyar Samar Da Nagartaccen Mulki A Arewa
Aruwan ya ce, “A bisa ga bayanan da rundunar ta bayar, sojojin a karkashin Operation Forest Sanity sun fara aikin share fage daga Damba zuwa Kangon Kadi, inda suka yi luguden wuta kan wasu ‘yan bindiga da aka gano a kusa da dajin Kangon Kadi, Labi da kuma kogin Udawa.
“’Yan bindigar sun gudu daga yankin Kangon Kadi a karkashin ingarmar karfin sojojin, inda suka bar mutane shida da suka yi garkuwa da su a sansaninsu.
“Sojoji ne suka ceto wadanda abin ya shafa.”
Kwamishinan ya ce, gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i, ya mima godiya tare da yaba wa sojojin bisa ci gaba da jajircewarsu a bangarori da dama.
Aruwan ya kara da cewa “Za a yi wa jama’a bayani kan ci gaban da aka samu.”