Hedikwatar tsaro ta ƙasa (DHQ) ta ce sojoji sun ceto mutane 117 da aka yi garkuwa da su tare da kama mutane 150 da ake zargi da laifuka a faɗin ƙasar nan cikin mako ɗaya.
Mai magana da yawun hedikwatar, Manjo Janar Markus Kangye, ya ce waɗanda aka kama sun haɗa da ‘yan ta’adda, masu satar mai, da sauran masu laifi.
- Masanan Kimiyya Na Kasar Sin Sun Samu Nasara A Bangaren Fasahar Sadarwar 6G Mai Amfani Da Haske Da Lantarki
- Yadda Kasar Sin Ta Nuna Wa Afirka Asalin Ma’Anar Hakkin Dan Adam Sabanin Irin Na Kasashen Yamma
Ya ƙara da cewa, wannan kame ya bai wa manoma damar yin noma cikin kwanciyar hankali.
A Arewa maso Gabas, sojoji sun kama masu taimaka wa ‘yan ta’adda 11, sun ceto mutane biyar sannan wani ɗan ta’adda ya miƙa wuya a Jihar Borno.
Hakazalika, suk ƙwato makamai, kuɗi, babura da motoci.
A Arewa maso Yamma, an kama ‘yan ta’adda 35 kuma an kuɓutar da mutane 76.
A Arewa ta Tsakiya, an kama mutane 49, an ceto mutane 36, yayin da a Kudu maso Gabas aka kama mambobin IPOB tara.
A Kudu maso Kudu, sojoji sun kama mutane 48, sun lalata wuraren tace ɗanyen mai, tare da ƙwato ɗanyen mai da dizal da kuɗinsu ya kai sama da Naira miliyan 443.
Janar Kangye ya tabbatar da cewa, za su ci gaba da kai irin waɗannan hare-hare domin tabbatar da tsaro a faɗin ƙasar nan.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp