Dakarun Sojin Nijeriya sun ceto mutane shida da aka sace a yankin dajin Ejiba–Saminaka da ke tsakanin Yagba Gabas da Yagba Yamma a Jihar Kogi.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, Laftanar Hassan Abdullahi, ya ce aikin ceton ya kasance wani ɓangare na yaƙi da ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane a jihar.
- Gwamna Otti Ya Ziyarci Nnamdi Kanu A Gidan Yarin Sakkwato
- ’Yan Bindiga Sun Kai Wa Ayarin Gwamnan Abia Hari A Imo
Ya ce maharan sun sako mutanen ne bayan matsin lamba da sojojin suka dinga yi musu ta sama da ƙasa tare da taimakon jirgin ’yansanda.
An riga an miƙa mutanen biyar ga iyalansu, yayin da mutum na shida ke karɓar magani saboda halin da yake ciki lokacin da aka ceto shi.
Rundunar Sojin Nijeriya ta tabbatar wa jama’a cewa za ta ci gaba da kare rayuka da dukiyoyinsu a jihar, tare da tarwatsa maɓoyar ’yan ta’adda.














