Rundunar Sojin Nijeriya sun ceto mutane tara da ‘yan bindiga suka sace a ƙaramar hukumar Patigi ta Jihar Kwara.
An ruwaito cewa an sace mutanen ne a ƙauyen Matokun da ke cikin Patigi.
- Ma’aikatar Kasuwancin Sin Ta Yi Kira Ga Amurka Da Ta Shiga Tattaunawar Cinikayya Da Sahihiyar Zuciya
- Kotu A Kano Ta Tsare Wani Mai Gidan Marayu Bisa Zargin Satar Yara Da Safararsu Zuwa Delta
Majiyoyin tsaro sun ce an miƙa waɗanda aka ceto ga shugaban ƙaramar hukumar Patigi, ta hannun Kakakin Majalisar, Mohammed Usman Alhaji.
An kai waɗanda aka ceto zuwa asibiti domin duba lafiyarsu.
Rundunar ta tabbatar da cewa za ta ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin jama’a a jihar.
Rundunar ta kuma yi alƙawarin ci gaba da aikin ceto har sai duk waɗanda aka sace sun kuɓuta kuma an dawo da zaman lafiya a jihar.
Mohammed Gana Alhaji, wanda ya yi magana a madadin al’ummar Patigi, ya gode wa sojojin bisa ƙoƙarinsu na yaƙi da rashin tsaro da kuma kare al’ummar yankin.
A ranar 23 ga watan Satumba, 2025, ‘yan bindiga sun kai mummunan hari wasu ƙauyuka na Patigi, inda suka kashe wata mata mai juna biyu a ƙauyen Matokun, suka yi wa wasu rauni, sannan suka sace mutum takwas.