Sojojin Nijeriya ƙarƙashin Shugaban Rundunar Operation haɗin kai a Arewa maso Gabas, Maj.-Gen. Waidi Shuaibu, ya miƙa wata ‘yar Chibok da aka ceto, Ihyi Abdu, ga Gwamnatin jihar Borno.
Ya zuwa yanzu dai an ceto ƴan matan Chibok 19 ta hanyar ɓarin wutar sojiji. Manjo Shuaibu ya jaddada ci gaba da ƙoƙarin Sojojin na ceto sauran ‘yan matan da ke hannun mayaƙan Boko Haram.
- Sojojin Sama Sun Yi Lugudan Wuta Kan Ƴan Ta’adda A Kaduna
- Ƴan Ta’adda 284 Sun Miƙa Wuya Ga Sojojin Haɗaka
Yayin bayyana yadda aka ceton tsohuwar ɗalibar, Manjo Haruna, wanda ke riƙe da muƙamin shugaban runduna ta7, ya yi bayani cewa an ceto Ihyi Abdu, tare da ‘ya’yan ta guda biyu, a ranar 23 ga Yuni yayin wani farmaki a dajin Sambisa. Ihyi, yanzu ta zama mai shekara 27, an yi garkuwa da ita a shekarar 2014 kuma an tilasta musu aure da ƴan Boko Haram, wanda ta zauna tare da shi a Garin Mustapha a cikin dajin Sambisa.
A halin yanzu, tana ɗauke da juna biyu na watanni uku kuma ta samu cikakken binciken lafiya tare da ‘ya’yan ta tun bayan ceto su.
Bugu da kari, an miƙa mutum 330 da aka ceto, wanda suka haɗa da mata 110 da Yara 220, ga Gwamnatin Jihar Borno.