Dakarun Sojin Nijeriya a Jihar Kaduna da ke aiki da bayanan sirri, sun yi kwanton bauna tare da kashe daya daga cikin ‘yan ta’adda dauke da makami a lokacin da yake hanyarsa ta kai wa al’umma hari a yankin Birnin Gwari na jihar.
Rundunar sojin ta bayyana hakan ne a ranar Laraba ta shafinta na X, cewa dakarun sun yi wa ‘yan ta’addan kwanton bauna a kusa da kauyen Kwaga a karamar hukumar Birnin Gwari, inda suka kashe daya yayin da sauran suka tsere da raunin harsashin bindiga.
- Da Ɗumi-ɗumi: Mataimakin Shugaban Ma’aikatan Jihar Legas, Soyannwo Ya Rasu Yana Da Shekara 55
- Matakin Amurka Na Kara Buga Harajin Kwastam Kan Hajojin Sin Babban Kurkure Ne
Sanarwar ta c, daukin gaggawar da sojojin suka kai ya hana kai hari kan jama’ar yankin da ba su ji ba ba su gani ba.
Sojojin sunyi nasarar kwato bindigu kirar AK-47 guda biyu da madaukan harsasai da kuma babura biyu a arangamar.
Sanarwar ta ce, a halin yanzu sojoji na ci gaba da da bin sahun sauran ‘yan ta’addan da suka tsere.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp