Dakarun sojin Nijeriya sun fatattaki wasu ‘yan ta’adda tare da kwato makamai da alburusai da shanun da aka sace a jihohin Borno da Katsina.
Rundunar ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da ta fitar a shafinta na X a ranar Laraba.
- Sojoji Sun Wanke Fursunoni 200 Da Ake Zargin Alaka Da Boko Haram A Borno
- Wang Yi Ya Gana Da Baki Amurkawa Bi Da Bi
Sanarwar ta ce sun kai farmakin ne wasu sansanonin ‘yan Boko Haram da kungiyar IS da ke yankin Gori a Karamar Hukumar Gwoza ta Jihar Borno.
Rundunar ta ce sojojin sun yi nasarar kashe dan ta’adda guda daya, tare da kubutar da shanu da dama tare da kwato bindiga kirar AK-47 guda biyu, alburusai da babur guda daya.
A Jihar Katsina, rundunar sojin ta ce wani samame da ta kai sansanin ‘yan ta’adda ya kai ga hallaka biyu a yankin Garin Rinji da ke Karamar Hukumar Batsari.
“Rundunar soji sun yi nasarar mamaye ‘yan ta’addan, inda suka lalata maboyarsu tare da kwato babura biyu da shanu 25 a yayin aikin.
“Sojoji har yanzu suna ci gaba da kai farmaki don kawar da ‘yan ta’adda a yankin baki daya.”