Rundunar Sojoji ta OPSH da ke sintiri a karamar hukumar Jos ta Kudu a ranar Litinin, 28 ga watan Afrilu 2025, sun harbe wasu mutune biyu da ake zargin barayin mota ne.
Wadanda ake zargin sun yi yunkurin sace wata mata mai launin toka (Ash), Opel Vectra a ƙofar Lalong da ke Jerin ginin gwamnatin tarayya, inda suka yi kokarin tserewa yayin da suka gamu da jami’an soji da ke kofar.
- Abubuwan Da Na Gani A Yankin ‘Hero Bay’ Da Ke Cikin Kasar China
- Arsenal Da PSG: Wa Zai Yi Nasara A Gasar Zakarun Turai A Yau?
A cewar sanarwar da mai magana da yawun rundunar, Major Samson Zhakom, ya fitar a ranar Talata, ya kara da cewa, daya daga cikin wanda ake zargin ya yi yunƙurin arcewa akan babur din jami’in soji yayin da ake tuhumarsa amma nan take aka harbe shi har Lahira.
Shi ma dayan, bayan ya bayyana cewa, sun kasance barayin mota ne a jihar Katsina amma wani abokinsu ya gayyace su zuwa jihar Filato domin ci gaba da sana’ar.
Yayin da ya amince zai jagoranci Tawagar Soji zuwa maboyarsu, jami’an sun gano bindiga kirar fistul daya da mukullai da suke amfani da su wajen bude motoci da gidajen jama’a, inda daga bisani shi ma ya yi kokarin arcewa kamar yadda abokin shi ya yi. Hakan ta sa shi ma aka harbe shi har lahira.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp