Dakarun Operation Haɗin Kai sun kai farmaki sansanonin Boko Haram a Tangalanga da Bula Marwa, tare da wasu wurare biyu da ke Jihar Borno.
Harin ya faru ne a ranar Lahadi, 7 ga watan Yuli, bayan da dakarun suka samu sahihin bayani cewa ‘yan ta’adda na gudanar da ayyukansu a yankin.
- UNHRC Ta Zartas Da Kudurin Sin Kan Kiyaye Hakkin Dan Adam Ta Hanyar Samun Ci Gaba
- Ƴan Bindiga Sun Kashe Mutane 13 A Neja
Da farko, sojojin sun isa Tangalanga inda ‘yan Boko Haram suka yi musu kwanton-ɓauna, amma sojojin suka yi gaggawar daƙile su kuma suka kashe mutum biyu daga cikinsu.
Daga nan ne suka samu wani bayani cewa akwai ƙarin ‘yan ta’adda da ke taruwa a garin Bula Marwa, sai suka wuce can.
Da sojojin suka isa Bula Marwa, ‘yan ta’addan da ke wajen suka tsere cikin dazuka.
Duk da haka, an kashe ɗaya daga cikinsu, sannan sojojin suka lalata wasu gine-gine da ke sansanin.
Abin farin ciki, babu wani soja da ya jikkata ko rasa ransa a wannan farmaki, wanda hakan ya ƙara musu ƙwarin gwiwa a yaƙin da suke yi da ta’addanci.
Sojojin sun ƙwato kayayyaki kamar bindiga AK-47 guda shida, alburusai 90 masu ɗango 7.62mm, da kuma tutar Boko Haram
Wannan nasara na daga cikin ci gaban da gwamnatin Nijeriya ke samu wajen fatattakar ‘yan ta’adda a Arewa Maso Gabas.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp