Rundunar Sojin Nijeriya ta kama wani ƙasurgumin mai garkuwa da mutane kuma dillalin makamai mai suna Buhari Umar, wanda ta addabi jihohin Gombe, Bauchi, Filato da Kaduna.
Daraktan hulɗa da manema labarai na rundunar tsaro, Manjo Janar Markus Kangye ne, ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da aka yi dangane da ayyukan rundunar a watan Afrilu.
- An Yi Taron Musayar Al’adu Da Cudanyar Jama’a Na Bikin Cika Shekaru 80 Da Nasarar Yakin Da Sinawa Suka Yi Kan Zaluncin Japan Da Yakin Ceton Kasa Na Tsohuwar Tarayyar Soviet
- Zamfara Ta Haɗa Gwiwa Da Oracle A Landan Don Bunƙasa Fasahar Matasa A Jiharta
A wani samame daban-daban, sojojin sun kama wasu mutane biyar da ake zargi da yin garkuwa da mutane a ƙaramar hukumar Lafia ta Jihar Nasarawa.
Waɗanda aka kama sun haɗa da Hassan Mohammed, Saleh Sani, Idi Yusuf, Adamu Danmai da Hassan Bello.
Hakazalika, sojojin sun kashe wasu daga cikin ‘yan haramtacciyar ƙungiyar IPOB, ciki har da ɗaya daga cikin shugabanninta Nkwachi Eze, wanda aka fi sani da “Onowu.”
Eze na cikin jerin da rundunar tsaro ke nema ruwa a jallo saboda hannu da yake da shi wajen kai hare-hare da garkuwa da mutane a yankin Kudu maso Gabas.
Manjo Janar Kangye, ya ƙara da cewa, a watan Afrilu, sojojin sun ceto mutane 173 da aka yi garkuwa da su, sannan sama da ‘yan ta’adda 204 da iyalansu sun miƙa wuya.
Haka kuma, sun kama mutane 430 da ake zargi da satar mai da wasu laifuka daban-daban.
A ƙarƙashin Operation DELTA SAFE, an daƙile satar mai da darajarsa ta haura Naira biliyan 1.9 a cikin mako guda.
Sun ƙwato sama da lita miliyan ɗaya ta ɗanyen mai da kuma dubban litoci na man fetur da wasu nau’inkan haramtattun mai.
Sojojin sun lalata wuraren tace ɗanyen mai da jiragen ruwa da kayan aiki daban-daban.
Har ila yau, sun gano manyan makamai da harsasai da abubuwan fashewa.
Wannan aikin na daga cikin ƙoƙarin gwamnati na yaƙar aikata laifuka da kare rayuka da dukiyoyin ‘yan Nijeriya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp