ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Tuesday, November 18, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Sojoji Sun Kama Masu Safarar Makamai Ga Ƴan Ta’adda

by Abubakar Sulaiman
1 year ago
Sojoji

Rundunar Sojojin Nijeriya tare da haɗin gwuiwar wasu hukumomin tsaro sun kama mutane 15 da ake zargin suna safarar makamai da kayan aiki ga masu ƴan ta’adda.

A sakamakon samun bayanan sirri, sojojin sun kai farmaki a wurare daban-daban, inda aka kama waɗannan mutane tare da kwace makamai da alburusai masu yawa. An kashe wani da ake zargin ɗan ta’adda ne yayin wani samame.

  • Sojoji Sun Sheƙe Ƴan Ta’adda Masu  Yawa A Kaduna Da Zamfara
  • Abin Da Ya Sa Muka Yi Zanga-Zanga A Kaduna -Masu Sharar Titi

A ranar 30 ga Agusta, 2024, an gudanar da wani samame a ƙauyukan Mararaba Donga da Manya a jihar Taraba, inda aka kama mutane biyar da ake zargi tare da kwace makamai da dama, ciki har da bindigogi kirar AK-47, bindigogin da aka ƙera da kuma alburusai da sauran kayan aiki.

ADVERTISEMENT

Haka zalika, an kama wasu mutum uku da ake zargin suna safarar kayan masarufi ga Boko Haram a jihar Yobe, inda suka shafe sama da shekaru biyu suna aiki tare da taimakon yan banga na yankin. Abubuwan da aka kwace daga hannunsu sun haɗa da motoci, babura, kayan gyaran babura, da kuma magunguna.

Bayan haka, an gudanar da wasu samame a jihar Kaduna inda aka kama wasu mutum huɗu da ake zargi suna safarar makamai da kayan aiki. Sojojin sun kwace alburusai, wayoyin hannu, katinan caji, da kuma kuɗi masu yawa.

LABARAI MASU NASABA

‘Yansanda Sun Kai Samame Maboyar ‘Yan Ta’adda, Sun Kwato Miyagun Kwayoyi A Gombe

Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

A jihar Edo, an kashe wani shahararren ɗan fashi yayin wani artabu, kuma a jihar Filato, an kama wasu mutum uku da ake nema ruwa a jallo kan sace-sace tare da makamai a hannunsu.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Da Ɗumi-ɗumi: ‘Yansanda Sun Tarwatsa Masu Zanga-zangar Adawa Da Dokar Ta-ɓaci A Ribas
Tsaro

‘Yansanda Sun Kai Samame Maboyar ‘Yan Ta’adda, Sun Kwato Miyagun Kwayoyi A Gombe

October 18, 2025
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja
Tsaro

Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

October 18, 2025
Sojoji Sun Kashe Kwamandan IPOB ‘Alhaji’, Da Wasu 26, Sun Kama 22
Tsaro

Sojoji Sun Kashe Kwamandan IPOB ‘Alhaji’, Da Wasu 26, Sun Kama 22

October 12, 2025
Next Post
Da Yiwuwar A Rage Wa Ƴan Majalisa Albashi

Da Yiwuwar A Rage Wa Ƴan Majalisa Albashi

LABARAI MASU NASABA

Bukatar Samar Da Cikkakken Tsaro Ga Hukumar Zabe

’Yansanda Sun Tura Tawaga Don Ceto Ɗaliban Da Aka Sace A Kebbi

November 18, 2025
Gwamnatin Sin Ba Ta Taba Bukatar Kamfanoni Su Tattara Ko Adana Bayanai Ba Bisa Ka’ida Ba Kuma Ba Za Ta Yi Hakan Ba 

Gwamnatin Sin Ba Ta Taba Bukatar Kamfanoni Su Tattara Ko Adana Bayanai Ba Bisa Ka’ida Ba Kuma Ba Za Ta Yi Hakan Ba 

November 17, 2025
Adadin Motocin Da Sin Ke Fitarwa Waje Ya Karu Da Kashi 15.7 Cikin Watanni 10 Na Farkon Bana

Adadin Motocin Da Sin Ke Fitarwa Waje Ya Karu Da Kashi 15.7 Cikin Watanni 10 Na Farkon Bana

November 17, 2025
Farashin Kayan Abinci Na Cigaba Da Sauka A Jihohin Arewa Maso Gabas

Farashin Kayan Abinci Na Cigaba Da Sauka A Jihohin Arewa Maso Gabas

November 17, 2025
An Bude Taron Tattaunawa Kan Wayewar Kai Tsakanin Sin Da Kasashen Larabawa Karo Na 11 A Beijing

An Bude Taron Tattaunawa Kan Wayewar Kai Tsakanin Sin Da Kasashen Larabawa Karo Na 11 A Beijing

November 17, 2025
NBS

Hauhawar Farashin Kayayyaki A Nijeriya Ta Ragu Zuwa Kashi 16.065%

November 17, 2025
Firaministan Sin Ya Isa Rasha Domin Halartar Taron SCO

Firaministan Sin Ya Isa Rasha Domin Halartar Taron SCO

November 17, 2025
‘Yansanda Sun Tsaurara Tsaron Iyakokin Kano Bayan Hare-haren ‘Yan Bindiga 

‘Yansanda Sun Tsaurara Tsaron Iyakokin Kano Bayan Hare-haren ‘Yan Bindiga 

November 17, 2025
Kudaden Kasafin Kudin Sin Sun Karu Da Kashi 0.8 Cikin Watanni 10 Na Farkon Bana

Kudaden Kasafin Kudin Sin Sun Karu Da Kashi 0.8 Cikin Watanni 10 Na Farkon Bana

November 17, 2025
Rashin Tsaro: Atiku Ya Yi Allah-wadai Da Harin Makarantar ‘Yan Mata Ta Kebbi

Rashin Tsaro: Atiku Ya Yi Allah-wadai Da Harin Makarantar ‘Yan Mata Ta Kebbi

November 17, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.