Sojojin Nijeriya a ƙarƙashin Operation ACCORD III sun kashe wani fitaccen shugaban ƴan ta’adda mai suna Babangida Kachala a jihar Kogi. Wannan na zuwa ne bayan samun bayanan sirri da aka samu kan motsin ƴan ta’adda a dajin Ofere da yankin Ayetoro Gbede.
Bayanin da Mataimakin Daraktan hulɗa da jama’a na Sojoji, Laftanar Hassan Abdullahi, ya fitar ya ce, dakarun sun kafa shingen kwanton-ɓauna, amma daga bisani su ma ’yan ta’addan suka yi musu kwanton-ɓauna yayin da suke komawa sansani. A fafatawar da ta biyo baya, Sojojin suka yi amfani da ƙarfin makamai suka halaka ɗaya daga cikin ’yan ta’addan.
- Rashin Tsaro: Zanga-zanga Ta Ɓarke A Jihar Kogi
- Gwamnatin Kogi Ta Jaddada Aniyar Magance Ambaliya Da Zaizayar Ƙasa
Binciken da aka yi a wurin ya tabbatar da samun sinƙin harsashin bindiga mai ɗauke da harsasai, da wayoyin salula 31, da na’urar duba hawan jini, da kwayoyin Tramadol, da guraye da layu, da kuma kuɗi Naira 16,000. An kuma gano jini a wurin da ke nuna cewa wasu daga cikin ’yan ta’addan sun tsere da raunukan harbin bindiga, ciki har da Babangida Kachala wanda daga bisani aka tabbatar da mutuwarsa.
Sojojin sun bayyana cewa za su ci gaba da sintiri da kwanton-ɓauna a yankin domin kawar da sauran ƴan ta’addan baki ɗaya. Rundunar ta ƙara tabbatar da cewa ƙarfinsu da ƙwarin gwuiwarsu na nan daram, tare da kira ga al’umma da su ci gaba da ba su bayanai masu inganci domin tabbatar da zaman lafiya a jihar Kogi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp