Sojoji sun kashe ƙasurgumin ɗan ta’adda kuma mai safarar makamai, Abu Mosaje, a Barkin Ladi, a Jihar Filato, tare da kama wasu masu safarar makamai uku a jihohin Filato da Kaduna.
An kama wani ƙasurgumin mai garkuwa da mutane Babangida Gora Usman, a Sanga, a Jihar Kaduna, yayin da aka kama wani mai safarar makamai, Timothy Yusuf, da ɗansa.
- INEC Ta Goge Sunayen Matattu 7,746 Daga Rajistar Zabe
- Manufofin Hulda Da Kasashen Wajen Da Nijeriya Ke Bukata
A Kudu maso Gabas, sojoji sun kama mambobin ƙungiyar IPOB guda bakwai, ciki har da wani mai garkuwa da mutane da masu bayar da bayanai, a Enugu da Imo.
Sojoji sun kashe ‘yan ta’adda 79, sun kama mutane 224, sun ceto mutane 67, tare da kama masu satar man fetur 28.
Haka kuma, sun lalata wuraren tace haramtaccen mai guda 42 kuma sun ƙwato kayan sata da darajarsu ta kai sama da Naira miliyan 747, ciki har da lita 842,685 na ɗanyen mai.
Sojojin sun ƙwace bindigogi 104, harsasai 1,953, babura, motoci, da sauran kayayyaki a yayin aikinsu.