Sojojin haɗin gwuiwa ta Operation MESA ƙarƙashin Birgediya ta 3 sun kashe ƴan bindiga 19 a ƙaramar hukumar Shanono ta jihar Kano, bayan wata musayar wuta mai tsanani da ta faru a yankunan Unguwan Tudu, Unguwan Tsamiya, da Goron Dutse da misalin ƙarfe 5:00 na yamma ranar Asabar. Wannan sumame ya biyo bayan sahihan bayanan leƙen asiri kan motsin wasu ƴan ta’adda da suka shiga yankin daga maƙwabtan dazuka.
A cewar sanarwar Kyaftin Babatunde Zubairu, Mataimakin Daraktan hulɗa da Jama’a na Birgediya ta 3, Sojojin tare da jami’an tsaro sun fatattaki ƴan ta’addan bayan musayar wuta, inda aka kashe ƴan bindiga 19, yayin da wasu suka gudu da raunin harbi. Ya ce an ƙwato babura da dama da kuma wayoyi guda biyu da aka samu a wajensu.
- Mayar Da Martani Kan Barazanar Amurka Ga Nijeriya: Fadar Shugaban Ƙasa Ta Yaba Wa Kwankwaso
- Kano Ta Amince Da Naira Biliyan 8.2 Don Ayyukan ilimi, Samar Da Ruwa, Da Makamashi
Sai dai, Sojoji biyu da jami’in sa-kai ɗaya sun rasa rayukansu yayin arta. Kyaftin Zubairu ya bayyana cewa sadaukarwar su hujja ce ta kishin ƙasa da jajircewar rundunar wajen kare ƴan Nijeriya da kawar da barazanar ta’addanci a yankin.
Kwamandan Brigade ta 3, Brigediya Janar Ahmed Tukur, ya yaba wa dakarun bisa jarumtarsu, yana mai tabbatar da cewa rundunar za ta ci gaba da gudanar da aikace-aikacen tsabtace yankin domin hana ramuwar gayya da kare al’ummomin da ake yawan kai wa hare-hare. Ya kuma shawarci mazauna yankin da su ci gaba da lura da duk wani motsi na baƙuwar fuska da ba a saba gani ba tare da sanar da jami’an tsaro cikin lokaci.














