Dakarun rundunar hadin gwiwa ta ‘Operation Hadarin Daji’ sun kashe wani dan bindiga tare da ceto mutane 15 da aka sace a Jihar Zamfara.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in yada labarai na rundunar, Laftanar Sulaiman Omale ya fitar a Gusau a ranar Talata.
- NiMet Ta Yi Hasashen Bullar Zazzabin Cizon Sauro A Watan Maris Da Afrilu
- An Kama ‘Yan Sintiri 10 Kan Zargin Kashe Limamin Garin Mada
“A wani artabu da aka yi, dakarun Operation Hadarin Daji sun hallaka wani gagarumin dan bindiga a yankin Tsohuwar Tasha da ke Karamar Hukumar Kaura Namoda a Jihar Zamfara.
“A ranar 5 ga watan Maris, 2024, sojojin sun yi artabu da ‘yan bindiga.
Omale ya ce, “A yayin artabun, maharan sun gudu, sojojinmu sun kashe daya daga cikin maharan a hanyarsu ta tserewa zuw daji.”
A cewarsa, wadanda aka sace sun hada da mata takwas da maza bakwai.
“Zaman lafiya ya daidaita a yankin zuwa yanzu, tare da samun kwarin gwiwar ci gaba da sintiri.
Omale ya kara da cewa, “Sojojin na cikin shirin ko-ta-kwana, cikin shiri.”
Tuni, Manjo Janar Godwin Mutkut, babban kwamandan runduna ta 8 na rundunar sojojin Nijeriya da ke Sakkwato, ya yaba da kwazon da kuma jajircewar sojojin.
Mutkut ya bukace su da su dage wajen samar da zaman lafiya a yankin Arewa maso Yamma da kuma fadin Nijeriya.