Dakarun Rundunar haɗin Gwuiwa ta Kasa da Kasa (MNJTF) da ke aiki a Ƙaramar Runduna ta 2 a Tsibirin Koulfoua, cikin yankin tafkin Chadi, sun daƙile wani mummunan hari da ‘yan ta’addan Boko Haram da ISWAP suka kai, wanda ya kai ga kashe kwamandansu, Amir Dumkei.
A cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na MNJTF, Laftanal Kanal Olaniyi Osoba ya fitar, ya bayyana cewa Sojojin sun kashe wasu ‘yan ta’adda guda biyar a fafatawar.
Ya ce lamarin ya faru ne a bakin ruwan Koulfoua, inda dakarun suka fatattaki ƴan ta’addan da Lugudan wuta, suka kuma kwato bindigogi AK-47 guda tara, jiragen ruwa uku da kuma tarin harsasai daga hannun su.
Osoba ya ƙara da cewa ‘yan ta’addan ISWAP da Boko Haram sun fara harin ne da safiyar Talata, 15 ga Yuli, 2025, inda suka kai farmaki kan sansanin sojin MNJTF da ke Tsibirin Koulfoua, amma suka gamu da ruwan wuta mai tsanani daga hannun dakarun rundunar.
Bayan artabu mai ƙarfi da harbin manyan makamai, kwamandan ‘yan ta’addan tare da wasu biyar sun mutu, yayin da sauran suka tsere da raunukan harbin bindiga. Rundunar ta kuma kwato tarin makamai daga hannunsu, yayin da ake ci gaba da farautar sauran da suka tsere.
Kwamandan MNJTF, Manjo Janar Godwin Mutkut, ya yabawa dakarun bisa juriyarsu da ƙoƙarinsu na kawar da ta’addanci a yankin tafkin Chadi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp