Sojojin rundunar 12 na rundunar Sojin Nijeriya sun kashe wani shahararren shugaban ƴan bindiga, Kachalla Balla, tare da wasu mabiyansa guda biyar a lokacin wani samame da ake ci gaba da gudanarwa a jihar Kogi.
Jami’in hulɗa da jama’a na bataliya ta 12, Laftanar Hassan Abdullahi, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar a Lokoja ranar Lahadi. Ya ce an kashe Kachalla Balla ne a ranar 5 ga Satumba, yayin musayar wuta da Sojojin suka yi da ƴan bindigar a mafakar su da ke kusa da Tunga, a ƙarƙashin aikin Operation EGWUA A TITE II.
- Gwamnatin Kogi Ta Jaddada Aniyar Magance Ambaliya Da Zaizayar Ƙasa
- Peng Liyuan Da Matan Shugabannin Kasashe Membobin SCO Masu Halartar Taron SCO Sun Ziyarci Kogin Haihe Na Tianjin
Abdullahi ya bayyana cewa Sojojin, tare da haɗin gwuiwar rundunar haɗaka (OHF), sun yi kwanton ɓauna a kan hanyar da ake zargin ƴan bindiga ke bi don samun kayan agaji a gadar Agbede–Adankoo (Mosalanci Boka). A wurin, an kashe wani ɗan leƙen asirinsu, tare da kwace babur, da wayoyi biyu, da sinƙin harsashin bindiga AK-47 mai ɗauke da harsasai 20.
A wani sumame makamancin haka, sojojin Bataliya ta 126 sun yi artabu da ƴan bindiga a cikin garin Tunga, inda suka kashe biyu daga cikinsu. Daga bisani, kwamandan, Birgediya Janar Kasim Umar Sidi, ya jagoranci wani farmaki, inda aka lalata sansanonin ƴan bindiga da dama.
Haka kuma, a ranar 2 ga Satumba, da taimakon jiragen yaƙi na 405, an kai hari kan ƴan bindiga a Ankomi, inda aka kashe da dama daga cikinsu. A tsakanin 3 zuwa 4 ga Satumba kuma, Sojoji sun yi bincike a Aleke, Ungwan Soni da Ungwan Nyaba, inda suka ceto wani mai suna Pabo Suleiman tare da ƴaƴansa biyu.
Abdullahi ya tabbatar da cewa rundunar Sojin Nijeriya za ta ci gaba da aiyukanta don kawar da ƴan bindiga da sauran barazanar tsaro a jihar Kogi da kewaye.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp