Rundunar Sojin Nijeriya ta tabbatar da kashe riƙaƙƙen shugaban ‘yan ta’adda, Yellow Danbokolo, a Jihar Zamfara.
Hedikwatar Tsaro ta ce Danbokolo ya mutu ne bayan samun raunin harbin bindiga a wani hari da dakarun Operation FASAN YAMA suka kai tare da haɗin gwiwar jiragen sojin sama da sauran hukumomin tsaro.
- Manomi Ya Ceto Jaririya Da Aka Binne Da Ranta A Kebbi
- Faɗuwar Darajar Naira Ta Sa Bashin Nijeriya Ya Ƙaru Zuwa Naira Tiriliyan 149
Danbokolo ya mutu sakamakon raunin da ya samu yayin musayar wuta da sojojin, inda wasu ‘yan ta’adda da dama suka baƙunci lahira.
Manjo Janar Markus Kangye, mai magana da yawun rundunar tsaro, ya bayyana cewa wannan aikin ya biyo bayan sahihan bayanan sirri, inda sojoji suka farmaki ‘yan ta’addan yayin da suke ƙoƙarin tserewa.
Ya ce Yellow Danbokolo ya daɗe yana addabar al’ummar Gabashin Sakkwato.
Ya samu munanan raunuka a harin da aka kai masa, wanda daga baya ya mutu.
Janar Kangye ya ƙara da cewa Danbokolo ya fi Bello Turji tsabibanci, shi ne ya jagoranci harin watan Disamban 2021 a ƙaramar hukumar Shinkafi ta Jihar Zamfara, inda ya ƙone fasinjoji da ransu a cikin mota.
Hakazalika, ya bayyana cewa Danbokolo na amfani da wata ƙwaya mai suna ‘pentazocine’ domin ci gaba da aikata miyagun laifuka.
Yanzu haka, sojojin Operation FASAN YAMA suna ci gaba da neman Bello Turji wanda ya ɓuya.
Janar Kangye ya tabbatar da cewa rundunar sojin Nijeriya tana da ƙwarin gwiwar samar da zaman lafiya a dukkanin sassan ƙasar nan.
Ya kuma roƙi haɗin kan ‘yan Nijeriya don cimma wannan buri.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp