Sojojin rundunar haɗin gwiwa ta Operation Enduring Peace sun samu nasara a kan ‘yan ta’adda a jihohin Kaduna da Filato, inda suka kashe wasu masu garkuwa da mutane tare da ceto waɗanda suka sace.
Rundunar sojin ta ce an gudanar da ayyukan ne tsakanin ranakun 11 zuwa 13 ga watan Disamba, bisa bayanan sirri da aka samu kan garkuwa da mutane da shirye-shiryen kai hare-hare a wasu yankuna.
- Sin Ta Dauki Matakan Kakkaba Takunkumi Kan Tsohon Shugaban Rukunin Tsaron Kasar Japan
- Nauyin Dukkanin Kasashe Ne Jan Hankalin Japan Ta Kawar Da Ragowar Masu Ra’ayin Amfani Da Karfin Soji
A Jihar Kaduna, sojoji sun kai samame wuraren da masu garkuwa da mutane ke ɓuya a ƙananan hukumomin Jema’a da Zangon Kataf.
A yayin musayar wuta, an kashe masu garkuwa da mutane guda uku, yayin da wasu suka tsere da raunuka.
Haka kuma sojojin sun daƙile wani shirin kai hari, lamarin da ya tilasta wa masu laifin tserewa.
A Jihar Filato kuwa, sojoji sun tare wani ƙasurgumin ɗan bindiga da mai garkuwa da mutane a Ƙaramar Hukumar Bassa.
Mutumin yana hango sojoji ya fara buɗe wuta, amma an kashe shi nan take. An ƙwato makamai, harsasai, wayar salula da kuɗi.
A wani aiki na daban a Filato, sojoji sun kai ɗauki bayan sace wasu mutane huɗu.
Bayan musayar wuta, an kashe ɗan bindiga guda ɗaya, sannan aka ceto mutanen lafiya.
An riga an mayar da waɗanda aka ceto hannun iyalansu, yayin da sojoji suka ce suna ci gaba da farautar sauran waɗanda suka tsere domin tabbatar da zaman lafiya a yankin.














