Gwamnatin Jihar Kaduna, a ranar Talata, ta tabbatar da cewa dakarun sojin Nijeriya sun kashe ‘yan bindiga da dama yayin da suka dakile wani hari a yankunan Idasu, Fatika da kuma dajin Makera a karamar hukumar Giwa.
Samuel Aruwan Kwamishinan Ma’aikatar Tsaro da Harkokin Cikin Gida ta Jihar Kaduna, ne ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata.
- An gudanar da taron tunawa da marigayi Jiang Zemin
- Portugal Ko Switzerland, Wa Za Ta Kai Bantenta Bayan Morocco Ta Lallasa Spain?
A cewarsa, martanin da gwamnatin Jihar Kaduna ta gudanar, ya nuna cewa an kashe ‘yan bindiga da dama.
Ya ce har yanzu wasu sun gudu da raunukan harbin bindiga a yankin Hayin Siddi da ke kan iyakokin jihohin.
Ya ce gwamnatin Jihar Kaduna ta lura da rahoton da gamsuwa, kuma ta yaba wa sojojin sosai kan nasarar da aka samu, sannan ya bukace su da su kara kaimi domin kamo wadanda suka samu raunuka.
A cewarsa, gwamnatin jihar ta yi kira ga ‘yan kasa a wadannan yankuna da su kai rahoton wasu mutane da ake tuhuma da ke neman kulawar jinya sakamakon harbin da jami’an tsaro suka samu.
Sanarwar ta kara da cewa, “Ana ci gaba da kai hare-hare a yankin gaba daya, kuma za a sanar da mutane abin da ake ciki.”