Akalla ‘yan ta’adda 51 ne sojoji suka kashe yayin da aka kama 93 da ake zargi da aikata laifuka a yankunan Arewa Maso Gabas a tsakanin 18 ga Mayu zuwa 1 ga Yuni, 2023.
Har ila yau, ‘yan Boko Haram 876 tare da iyalansu sun mika wuya ga sojojin da ke Borno.
- NAHCON Ta Bai Wa Alhazan Jigawa Tabbacin Sauka Lafiya
- Hadarin Mota Ya Ci Rayukan Mutane Takwas, 6 Sun Jikkata A Hanyar Bauchi
Daraktan ayyukan yada labarai na tsaro, Manjo Janar Musa Danmadami ne, ya bayyana hakan yayin taron tattaunawa na mako biyu kan ayyukan sojoji a fadin kasar nan.
Danmadami, ya ce an kashe ‘yan ta’addan ne a yayin farmakin da suka kai wasu yankunan biyu, ya kuma kara da cewa an kama wasu ‘yan ta’addan guda 22 da ke safarar makamai.
Ya ce, “Sojoji sun kuma kashe ‘yan ta’addar Boko Haram 26 da suka hada da ‘yan kunar bakin wake guda daya, sun kama wasu 22 da ke safarar makamai tare da kama dan Boko Haram guda daya dauke da makamai.
“Sojoji sun yi nasarar kubutar da fararen hula 16 da aka yi garkuwa da su, yayin da ‘yan ta’addar Boko Haram 876 da suka hada da manya maza 89, manyan mata 249, da kananan yara 538 suka mika wuya ga sojoji.
“Haka kuma, sojoji sun kashe ‘yan ta’adda 25, sun kama mutane 41 da ake zargi da aikata laifuka, tare da ceto fararen hula 36 da aka yi garkuwa da su a yankin Arewa Maso Yamma.”
Ya kuma kara da cewa, an mika duk wasu kayayyakin da aka kwato na wadanda ake zargi, da kuma ceto fararen hula da aka yi garkuwa da su, an mika su ga hukumar da ta dace domin ci gaba da daukar mataki na gaba.