Dakarun rundunar sojin Nijeriya sun kashe ‘yan ta’adda 624, sun kuma kama 1,051 ciki har da masu kai musu rahoto, sannan sun ceto mutane 563 a watan Mayu, 2024.
Daraktan yada labarai na tsaro, Manjo Janar Edward Buba ne, ya bayyana hakan ga ‘yan jarida a Abuja.
- ‘Yancin Kananan Hukumomi: Kotun Koli Ta Bai Wa Jihohi 36 Kwana 7 Su Kare Kansu
- Ina Kokarin Cika Alkawuran Da Na Dauka – Tinubu
Ya kuma yi kira ga ‘yan Nijeriya da su kasance masu goyon bayan sojoji wajen yaki da ta’addanci da ‘yan fashi da sauran laifuka daban-daban.
Buba ya sake nanata cewa al’ummar kasar nan na da irin rawar da za su taka wajen kawo karshen hare-haren ta’addancin a fadin kasar nan.
Kakakin tsaron ya kuma bayyana cewar dakarun sun kwato makamai guda 707.
Ya ce sun kuma gano bindigogi kirar AK-47 guda 411 da kananan bindigogi guda 234 da sauran muggan makamai.
Ragowar kayayyakin da aka kawo ma sata sun hada da litar mai 4,871,470 da danyen mai lita 931,416, in ji Manjo Janar Buba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp