Yayin da Rundunar Sojojin Saman Nijeriya ke kara kai hare-hare a yankunan ‘yan ta’adda, dakarun rundunar Birget ta 1, Rundunar hadin gwiwa ta Arewa maso Yamma, tare da Operation Fansan Yamma sun kashe ‘yan ta’adda da dama ciki har da wani dan ta’adda mai suna Sani Rusu tare da kwato makamai a jihar Zamfara.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ‘Operation Fansan Yamma’, Laftanar Kanar Abubakar Abdullahi, ya rabawa manema labarai a Gusau ranar Litinin.
- Da Ɗumi-ɗumi: Jami’an Tsaro Sun Kashe ‘Yan Bindiga 80 A Katsina
- Na Ɗauki Rarara Tamkar Mahaifi A Wajena – Tijjani Asase
Sanarwar ta ce, sojojin sun kai samame ne a kauyen Bamamu da ke karamar hukumar Tsafe a ranar Asabar 4 ga watan Janairu, 2025 inda suka yi taho mu gamu da ‘yan ta’addan.
A arangamar, Sojojin sun yi nasarar kawar da wani fitaccen dan bindiga, tarwatsa matsugunansu tare da kwato tarin makamai.
Hakazalika, sanarwar ta kara da cewa, a wani samame na daban, rundunar sojin sama ta Operation Fansan Yamma ta kai farmaki ta sama kan ‘yan ta’addan da suka hadu a tsakanin Fakai da Kware a karamar hukumar Shinkafi a ranar 30 ga watan Disamba 2024.
“An kaddamar da wannan harin ta sama ne a matsayin martani ga bayanan sirri da ke nuni da cewa ‘yan ta’adda a karkashin jagorancin Bello Turji sun gudanar da taro a yankin.
Sanarwar ta kara da cewa, “Sojojin sun kuma kai farmaki kan sansanin Bello Turji da ke yankin Chida a Shinkafi a ranar 5 ga watan Janairun 2025. Binciken jirgin yakin ya nuna cewa, an yi wa ‘yan ta’addan mummunar barna a wadannan hare-hare tare da jikkata ‘yan ta’adda da dama inda aka tarwatsa maboyarsu.”