Hedikwatar Tsaro ta Kasa, ta ce dakarun Operation Forest Sanity da ke sintiri a maboyar ‘yan bindiga a kauyen Danmarke da ke karamar hukumar Gummi a Jihar Zamfara, sun ceto wasu mutane uku da aka yi garkuwa da su tare da kwato makamai da babura 30.
Daraktan yada labarai na tsaro, Manjo Janar Musa Danmadami, ya ce sojoji a yayin farmakin sun yi artabu da ‘yan ta’addan wanda hakan ya sa suka tsere daga maboyarsu.
- Kasar Sin Tana Goyon Bayan Bukatar Kasashe Masu Tasowa Game Da Kudaden Tallafin Sauyin Yanayi
- Gwamna Buni Ya Gabatar Da Biliyan 163 A Matsayin Kasafin 2023 Ga Majalisar Dokokin Jihar Yobe
Ya ce yayin da wasu da dama suka gudu da raunukan harbin bindiga, sojojin sun yi amfani da yankin gaba daya tare da kubutar da mutane uku da aka yi garkuwa da su, sun kwato bindigogi kirar AK-47 guda biyar da babura 30 da dai sauransu.