Rundunar sojin Nijeriya ta bayyana a shirye ta ke ta saki fursunoni sama da 200 da aka tsare kan zargin alaka kungiyar Boko Haram.
Rundunar sojin ta wanke fursunonin da ta kama ne a samame daban-daban a wani shiri na yakar Boko Haram.
- Gwamnan Zamfara Ya Yi Kira A Kara Yawan Sojoji A Jihar Don Yaki Da ‘Yan Bindiga
- Gwamnatin Kaduna Ta Karɓi ‘Yansanda Masu Horo Na Musamman 200 Da Motocin Yaƙi 2
Leadership ta ruwaito yadda aka mika wadanda ake tsare din ga gwamnatin Jihar Borno kafin su koma cikin al’umma.
An yi bikin mika fursunonin ne gwamnatin Borno a barikin Giwa da ke Maiduguri, babban birnin jihar.
“A cikin mutane 200 wadanda ake zargin ‘yan Boko Haram ne da jami’an tsaro sun wanke su daga zargin aikata wani laifi, za a mika su ga gwamnatin Jihar Borno.
“An shirya bikin mika ragamar su a safiyar yau (Talata) da misalin karfe 10:00 na safe a barikin Giwa,” in ji sanarwar.
Sanarwar ta kara da cewa kwamishiniyar harkokin mata ta jihar, Zuwaira Gambo, da takwararta ta yada labarai da tsaron cikin gida, Farfesa Tar Umar ne, suka karbi wadanda aka wanke a madadin gwamnatin jihar.