Sojojin Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kwango (DRC) sun zargi kungiyar ‘yan tawayen M23 da kashe fararen hula a kalla 17 a wani hari da suka kai a yankin gabashin kasar mai fama da rikici.
Sanarwar da rundunar sojin ta fitar a jiya Litinin, ta ce an kai harin ne da yammacin ranar Asabar a Kauyen Munzinzi da ke yankin Walungu na lardin Kibu ta Kudu.
- Sojojin Sama Sun Yi Lugudan Wuta Kan Ƴan Ta’adda A Jihar Neja
- Yadda Tinubu Ya Karrama Sojojin Da Aka Kashe A Neja Delta
A cewar sanarwar, mayakan na M23 sun afka wa kauyen ne da misalin karfe 6:30 na yamma agogon kasar, inda suka kashe a kalla fararen hula 17 tare da cinna wa gidaje wuta.
Sanarwar ta ce mazauna kauyen da dama sun tsere zuwa wuraren da aka girke sojoji da ke kusa da su, domin tsira da rayukansu, kana ta kara da cewa mai yiwuwa an yi kisan ne a matsayin ramuwar gayya kan asarar da ‘yan tawayen suka tafka a fagen fama a baya-bayan nan.
Kungiyar M23 daya ce daga cikin kungiyoyi masu dauke da makamai a yankin, wacce take kai hare-hare a-kai-a-kai a lardunan Kibu ta Arewa da Kibu ta Kudu, lamarin da ya raba dubban daruruwan mutane da gidajensu tare da kazanta tabarbarewar al’amuran jin kai.














