Kasar Faransa ta kammala janye sojojinta bayan da sabuwar gwamnatin mulkin sojin Nijar ta bukaci su fice daga kasar.
Lamarin janyewar dai ya kawo karshen tallafin soji da Faransa ta kwashe shekaru ta na yi, tare da nuna damuwa daga manazarta dangane da gibin da ake samu a yakin da ake da mayakan yan ta’adda a yankin Sahel na Afirka.
- Mai Da Hankali Kan Kokarin Samar Da Ci Gaba Yana Karfafa Hulda Tsakanin Afirka Da Sin
- Firaministan Kasar Sin Ya Ziyarci Yankunan Da Suka Yi Fama Da Bala’in Girgizar Kasa
Jiragen saman sojojin Faransa na karshe sun bar Nijar a ranar 22 ga watan Disamba, wa’adin da gwamnatin mulkin sojin kasar ta kayyade, bayan juyin mulkin da aka yi a watan Yuli, kamar yadda babban hafsan sojin Faransa ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Associated Press.
Tuni Faransa ta sanar a wannan makon cewa za ta rufe ofishin diflomasiyyarta a Nijar har na tsawon wani lokaci.
Duk da haka, kasar za ta ci gaba da shiga cikin yankin Sahel, da ke kudu da hamadar Sahara wanda ya kasance wuri mai zafi ga masu tsattsauran ra’ayi – ko da yake ya sha bamban, in ji shugaba Emmanuel Macron yayin wata ziyara da ya kai wani sansani a Jordan.
“Na yanke shawarar wasu muhimman sake fasalin,” in ji Macron.
“Za mu ci gaba da kare muradunmu a can, amma sojojinmu ba za su kasance a can har dindindin ba, za su kasance masu zaman kansu,” in ji shi.
Majalisar mulkin Nijar ta bayyana kawo karshen hadin gwiwar soji da Faransa a matsayin mafarin sabon zamani ga ‘yan Nijar.