Dakarun sojin Nijar da suka yi juyin mulki sun bai wa ambasadan Faransa sa’o’i 48 da ya fice daga kasar, kamar yadda AFP ta ruwaito.
Hukuncin nasu ya umarci Sylvian Itte da ya fice daga kasar biyo bayan rashin halartar wani taro da aka gudanar a kasar.
- Gwamnatin Zamfara Za Ta Bai Wa Mata Fifiko Wajen Walwalarsu
- Ambaliya: NEMA Ta Bada Tallafin Kayayyakin Agaji Ga Mutane 22,202 A Kebbi
Wannan yunkurin na zuwa ne bayan da sojin kasar suka hambarar da gwamnatin shugaba Mohamed Bazoum tare da tsare shi tare da iyalansa.
Sojojin sun zargi Faransa da yunkurin dawo da shugaba Bazoum kan karagar mulki.
Don maida martani kungiyar ECOWAS ta sanya Nijar jerin takunkumai don sanya mata matsin lamba.
Faransa na da sojoji 1500 da ke Nijar don yaki da masu jihadi da kuma masu tsattsauran ra’ayi.