Tsohon gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce sojoji za su iya kawo karshen matsalar tsaron da suka addabi Nijeriya.
Jagoran jami’yyar NNPP na kasa, ya bayyana haka ne yayin wata zantawa da ya yi da manema labarai jim kaɗan bayan kammala taron kwamitin zartarwa na jami’yyar a Abuja.
- Bayar Da Tallafin Wutar Lantarki Kaso 85 na Kara Nuna Tinubu Mai Kishin Jama’a Ne – Minista
- Gwamnatin Jihar Kwara Ta Gargadi Manoman Kan Sayar Da Kayan Aikin Da Ta Ba Su
Ya ce duk da cewa hakkin gwamnatin tarayya ne, ta magance matsalar tsaro, amma ’yan Nijeriya na da muhimmiyar rawar da za su taka ta hanyar bai wa hukumomin tsaro muhimman bayanai.
Kwankwaso, ya kuma kara da cewa “A matsayina na tsohon ministan tsaro kuma tsohon babban jami’in tsaro na Jihar Kano na tsawon shekaru takwas, wanda ya yi gwagwarmayar siyasa, na yi imanin tukarar kalubalen tsaro na hannun gwamnatin tarayya.
“Kowa yana ganin yadda jihohi ke kirkiro jami’an tsaro. Wani lokaci abun ya ba ka dariya. A halin da ake ciki a Nijeriya sojoji ne kadai za su iya kawo karshen matsalar tsaro.”
Sannan ya ce dole ne kowa ya ba da hadin kai don ganin an samu zaman lafiya a Nijeriya.
“Wasu daga cikinmu da ke kauyuka suna ganin yadda mutanenmu suke zuwa gonaki. Yanzu kuma ba sa iya zuwa gona.
“Ana korar su daga kauyuka da garuruwansu. Masu laifi da ’yan bindiga suna sace ’ya’yanmu kullum, in ji shi.
Kwankwaso, wanda shi ne dan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NNPP a zaben 2023, ya ce jam’iyyarsa tana da tsarin da za ta bi wajen magance matsalolin da suka addabi Najeriya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp