Hedikwatar tsaro ta kasa ta ce dakarun Hadin Kai da Hadarin Daji sun kashe ‘yan ta’adda akalla 44 tare da kama sama da 50 a Arewa maso Gabas da Arewa maso Yamma a cikin mako biyu da suka gabata.
Daraktan ayyukan yada labarai na tsaro Musa Danmadami ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai da suka saba yi duk mako biyu kan ayyukan rundunar, ranar Alhamis a Abuja.
- Da Dumi-Dumi: An Harbi Tsohon Firaministan Pakistan, Imran Khan
- Kammala aikin tashar ruwa mai zurfi ta Lagos zai ingiza bunkasar tattalin arzikin Najeriya
A yankin Arewa maso Gabas, Mista Danmadami ya ce a tsakanin ranar 20 ga watan Oktoba zuwa ranar 2 ga watan Nuwamba, sojojin Operation Hadin Kai sun kama wasu mutane 27 da ake zargin ‘yan ta’addar Boko Haram ne da kuma mayakan ISWAP tare da kashe 19.
Mista Danmadami ya kara da cewa sojojin sun kwato manyan makamai da alburusai na nau’o’i daban-daban da kuma sauran kayan aiki a lokacin.
A cewarsa, a ranar 21 ga watan Oktoban da ya gabata ne, rundunar ta kai farmaki ta sama a kan ayarin motocin ‘yan ta’addan akan hanyar Tunbum Aliyu, kusa da tafkin Chadi, wurin da ‘yan ta’addan ke kudu maso yammacin Maiduguri.
Ya ce hare-haren sun kawar da ‘yan ta’adda da dama da kuma manyan motocin bindigu guda bakwai da sauran makamai.
“Hakazalika, bisa sahihin bayanan sirri na ‘yan ta’addan da ke yin sintiri a cikin unguwannin Abulum da Njibul da ke kusa da dajin Sambisa, rundunar ta kai farmaki a wuraren a lokaci daya tare da kawar da dimbin ‘yan ta’addan, yayin da aka ga wadanda suka samu raunuka sun yi kaca-kaca wasu kuma sun tsere.
“Hakazalika, sojojin tare da hadin gwiwar jami’an sa-kai a ranar 22 ga watan Oktoba, sun kama wani mutum da ake zargi da mallakar katin zabe guda 67 a sansanin ‘yan gudun hijira da ke garin Shuwari a karamar hukumar Maiduguri ta Jihar Borno.
“Haka kuma, a wannan sansani, an kashe wani sanannen dan ta’adda, Lawan Yashin, wanda ya yi yunkurin tserewa da ganin sojoji.
“A lokacin guda ‘yan ta’addar Boko Haram 145 da iyalansu da suka hada da manya maza 30, manya mata 33 da kananan yara 82 ne suka mika wuya ga sojoji a wurare daban-daban ga sojoji a Arewa maso Gabas,” in ji Danmadami.
A yankin Arewa maso Yamma, kakakin rundunar tsaron, ya ce dakarun hadin gwiwa na Hadarin Daji da Whirl Punch sun kashe ‘yan ta’adda 25, sun kama 18 tare da kubutar da fararen hula 19 a hare-hare daban-daban.
Mista Danmadami, ya ce sojojin sun kuma kwato manyan makamai da alburusai daban-daban da kuma shanu 441 da aka sace.
Ya kara da cewa sojojin a ranar 24 ga watan Oktoba, sun kai wa ‘yan ta’addan hari a kan hanyar Buruku-Angwan Yako-Udawa a karamar hukumar Chikun ta Jihar Kaduna, inda suka ceto fararen hula 10 tare da kwato motoci uku.
Kakakin rundunar, ya ce sojojin sun kuma kashe ‘yan bindiga biyu tare da kubutar da wasu mutane tara da aka yi garkuwa da su a Faskari a Jihar Katsina da kuma Anka a Zamfara.