Dakarun sojojin Nijeriya sun kai hari kan wani taron tattaunawa da kungiyar ‘yan ta’addar ISWAP ta shirya a tsakanin mambobinta, inda suka kashe ‘yan ta’addan da dama a jihar Yobe.
LEADERSHIP ta samu cewa ‘yan ta’addan sun hadu ne a wani wuri da ake kira Wulle a babura da motoci da nufin kai hari kan sansanin sojoji mafi kusa.
Wani rahoton leken asirin da Zagazola Makama, kwararre a fannin yaki da tada kayar baya kuma mai sharhi kan harkokin tsaro a tafkin Chadi ya samu daga manyan majiyoyin soji, sannan LEADERSHIP ta samu, ya bayyana cewa, a bisa bayanan sirrin, sojojin bataliya ta 27, sun harba rokoki da dama kan ‘yan ta’addan wanda hakan ya yi sanadiyyar kashe ‘yan ta’addan da ba a tantance adadinsu ba.
An kuma bayyana cewa daga baya ‘yan ta’addan sun dawo a kan babura shida da mota daya domin kwashe gawarwakin mutanen su.