Rundunar Sojan Saman Nijeriya (NAF), ƙarƙashin ɓangaren Operation Fansan Yamma, ta kai hare-haren sama a wasu ma’aajiyar makamai ta shugaban ‘yan ta’adda Ado Aleiro, tare da kashe mutane da dama a jihohin Kebbi da Zamfara.
Mai magana da yawun NAF, Air Commodore Olusola Akinboyewa, ya bayyana cewa waɗannan hare-hare sun zama wani ɓangare na atisayen Farautar Mujiya, don taimaka wa Sojojin ƙasa wajen magance laifuka a yankin Arewa maso Yamma.
- Ma’aikatan NAFDAC Sun Tsunduma Yajin Aiki
- NAF Ta Kashe ‘Yan Ta’adda Fiye Da 70 A Borno
NAF ta yi amfani da kayan leƙen asiri da kai hare-hare don kai farmaki a ranar 8 ga Nuwamba, 2024, a wurare kamar sansanin Sangeko a Zamfara, kusa da iyakar Kebbi, da sansanin Aleiro kusa da Asola Hill a Tsafe. Waɗannan hare-hare sun lalata manyan wuraren ajiyar makamai na Aleiro tare da raunana ƙarfin mayaƙansa.
Akinboyewa ya tabbatar da cewa hare-haren sun ba da damar da wasu mutane da aka sace suka tsere zuwa Kebbi. Ya ce waɗannan ayyukan sun ƙara wa mazauna yankin ƙwarin gwuiwa da kuma tabbatar da niyyar rundunar tsaron wajen tabbatar da tsaro a yankin.