Fitaccen ɗan gwagwarmaya kuma mai rajin kare haƙƙin jama’a, Omoyele Sowore, ya ziyarci Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara a gidan yarin Kuje da ke Abuja.
Sowore ya wallafa hotunan ziyarar a shainsa na Facebook, inda ya bayyana cewa ya je tare da Barista Hamza Nuhu Dantani.
- Ma’aikatar Tsaron Kasar Sin Ta Yi Allah Wadai Da Aniyar Amurka Ta Sayarwa Yankin Taiwan Makamai
- Wani Mai Taɓin Ƙwaƙwalwa Ya Kashe Soja A Legas
Ya ce an yanke wa Sheikh Abduljabbar hukuncin kisa a Kano a zamanin tsohon gwamna Abdullahi Ganduje bisa zargin ɓatanci, wanda ya ce hukuncin tsantsar siyasa ce.
Sowore ya nuna damuwa, yana cewa wasu na kusa da malamin sun taka rawa wajen ganin an tura shi gidan yari.
Ya ce sun same shi cikin ƙwarin guiwa, inda malamin ya bayyana cewa Allah ne yake tsare da shi kuma zai ci gaba da bin koyarwar Allah har ƙarshen rayuwarsa.
Sowore ya ce ya kamata a yi wa kowa adalci, sannan ya yi kira da a tabbatar da an yi wa Sheikh Abduljabbar adalci da kuma dakatar da amfani da addini wajen muradun siyasa.














