Abin ne ya zama wani lamarin wanda zai ci gaba da daure kai,da daukar hankalin al’umma dangane da abubuwan da suke faruwa a jami’ar Kalaba babban birnin Jihar Kuros Ribas, saboda kuwa ba sau daya ba ne aka samu irin wannan ya fara faruwa a jami’ar ba. Ranar Litinin ce hukumar yi wa kasa hidima ta soke satifiket wadanda suka yi wa kasa hidima, tsakanin shekarun 2021 da 2023 wadanda daga jami’ar ne suka kammala karatunsu har suka tafi zuwa shirin yi wa kasa hidima na su 101 wadanda suka shiga jami’ar, har suka kammala ba tare da sun cika ka’idoji ba.
Abin da ke daure kai su wanene ke da alhaki na tantance wadanda suka cancanci shiga jami’ar, hukumar kula da lamurran masu yi wa kasa hidima ce, ko kuma ita jami’ar, saboda idan aka duba wadanda suka yi aikin yi wa kasa hidima tsakanin shekarun 2021 da 2023 har sun kai yawan hakan, suka shiga jami’ar har suka kammala suka yi aikin yi wa kasa hidima amma ba a gane ba sai da suka riga suka kammala. A wannan shekarar ma an dade da amincewa da 54, wadanda tuni aka tura sunayensu wuraren da ya dace su je su yi zaman wata guda, amma an gano cewar basu cancanci hakan ba. Duk daga ita jami’ar ta Kalaba.
- Jawabin Tinubu Kan Kisan Sarkin Gatawa Ya Bar Baya Da Ƙura
- Mutum Miliyan 7.9 Da Ta’addanci Ya Tagayyara A Jihohi 3 Na Bukatar Agaji – UNOCHA
Gaba daya ke nan 155 wadanda suka halarci makarantar ta hanyar da bata kamata, suka kuma kammala ba a gano su ba, amma kuwa wannan lamari yana da ban mamaki. Me yake faruwa ne a ita jami’ar ta Kalaba sai kace ba Shugabnni? koda yake duk wannan ma somin tabi ne ko nace duk da zai dauki hankali, akwai ma wani wanda ke sayar da Biredi ya samu an sa sunan shi cikin wadanda za su tafi aikin yiwa kasa hdima da za a fara daga ranar 28 ga Agusta 2024.
Ya kamata a jinjina wa hukumar kula da masu yi wa kasa hidima a karkashi shugabancin Birgediya Janar YD Ahmed irin jan aikin da take yin a kawo gyara ta bangaren ilimi, musamman ma yadda take tsayawa kai da fata sai taga ana yi abubuwan da suka dace kamar yadda doka ta shimfida. Bugu da kari duk a cikin irin kokarin nata ta gano makarantu masu bada HND basu bin ka’ida ta sai an yi aikin sanin mamaki ana shekara daya, kafin a samu damar zuwa karatiun HND. Wadanda suka kammala irin makarantun basu da satifiket mai nuna sun yi aikin sanin makama na shekara daya, na cikin tsaka mai wuya dangane da zuwa NYSC.
Mai lura da yadda harkokin jami’ar ta Kalaba suke tafiya ritaya DIG Udom Edppoudom ya gode wa mataimakiyar shugabar jami’ar Farfesa Florence Obi, akan irin matakin da ta dauka wajen zuwa ofishin ta bashi labari,inda ta ce ta ga wasu sunayen daliban da basu kamata ace suna cikin ‘yan makarantar ba. Ita kuma ce ta sanar da hukumar kula da al’amuran masu yiwa kasa hidima akan sunayen wadanda basu cancanta ace sun yi karatu a makarantar ba ,amma har sun kammala har ma an tura sunayensu Jihohin da za su tafi aikin yiwa kasa hidimar.
Lokaci ya yi wanda za a hukunta mutane 155 wadanda suka yi Jami’ar ta hanyar da bata dace ba, da wadanda suka taimaka masu har suka samu damar, domin hakan ya zama izina ga wadanda suke yi asirinsu bai kai ga tonuwa ba, da kuma wadanda suka fara tunanin yin hakan.