Jami’an gwamnatin tarayya sun tarbi kashin na uku na ‘yan Nijeriya da aka kwaso daga Sudan zuwa Abuja a ranar Asabar.
A cewar hukumar ‘yan Nijeriya mazauna kasashen waje, wadanda aka dawo da su sun kunshi mutane 131 yawancinsu mata da kananan yara sun sauka a filin jirgin saman Nnamdi Azikwe da karfe 1:45 na safiya.
- Abin Da Ya Sa Wasu Manoma A Jihar Kano Suka Ba Da Hayar Gonakinsu
- Na Gwammace Zama Mashawarci A Gefe, Ba Shugaban Ma’aikatan Tinubu Ba – El-Rufai
Jami’an sun bayyana fatansu na ganin an kammala aikin cikin nasara.
Zuwan su ya zo ne bayan kashi na biyu na ‘yan kasar Sudan da suka isa Nijeriya a yammacin ranar Juma’a.
Kashi na biyu sun isa filin jirgin saman Abuja da misalin karfe 3 na rana dauke da mutane kusan 130 a cikin wani jirgin saman kamfanin Tarco Airline.
Da sanyin safiyar Larabar da ta gabata ne rukunin farko na ‘yan gudun hijira suka iso daga kasar da ke fama da yaki a arewacin Afirka.
Ana sa ran karin ‘yan Nijeriya za su iso nan da kwanaki masu zuwa yayin da ake sa ran wasu kamfanonin jiragen sama guda hudu da suka hada da Air Peace, da Max Air, da Azman Air, da kuma Tarco Aviation za su dawo da su gida Nijeriya.