Kashi na biyu na mutanen da aka kwashe sun kunshi ‘yan Nijeriya 130; mata 128 da maza biyu sun isa Abuja ta jirgin saman Tarco.
Da misalin karfe 4 na yamma wadanda aka kwaso suka isa filin jirgin.
- Qin Gang Ya Halarci Taron Ministocin Wajen Kasashen Kungiyar SCO
- Bukatar Tafiyar Da Tattalin Arzikin Nijeriya A Dunkule Ta Hanyar Rage Amfani Da Tsabar Kudi
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da babban daraktan hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa (NEMA), Mustapha Ahmed ya ce tuni wasu karin ‘yan Nijeriya 800 ke kan hanyarsu ta zuwa filin jirgin na Masar domin kwaso su zuwa Nijeriya.
Shugaban NEMA, wanda ya tarbi wadanda aka kwaso daga Sudan, ya ce Max Air mai daukar fasinjoji 560 da kuma Azman Air mai daukar fasinjoji 400 tuni suka isa kasar Masar domin jigilarsu.
Ya kuma ce an kulla alaka da jirgin Air Peace da gwamnatin tarayya za ta yi duk mai yiwuwa don kwaso dukkan ‘yan Nijeriya daga Sudan.
Wasu daga cikin wadanda aka kwaso, wadanda suka zanta da LEADERSHIP, sun ce abin ya yi muni matuka, amma sun ji dadin dawowarsu gida.
Daya daga cikinsu wata Hajia Medina ta ce ta yi balaguro zuwa tashar jiragen ruwa na Sudan da kan iyakar Masar cikin mawuyacin hali.
Sai dai ta yaba wa gwamnatin tarayya da ta kawo musu dauki.
Har ila yau, shugaban kafafen yada labarai na NEMA, Ezekiel Manzo ya ce, “Bugu da kari, bisa la’akari da muhimman bukatun al’ummar Nijeriya da ke kan iyakar Masar, NEMA ta ci gaba da samar musu da abinci da ruwa da sauran muhimman kayayyaki a yayin da suke jiran izinin shiga kasar Masar don jigilar su zuwa Najeriya.
“NEMA da Ofishin Jakadancin Nijeriya a Masar ne suka samar da abincin.
“Ta hanyar shigar da wasu kamfanonin jiragen sama, za a kara kaimi wajen kwashe su, haka zalika, Taco aviation da ke Sudan ta himmatu wajen inganta jigilar ‘yan kasarmu zuwa gida daga gabar tashar jiragen ruwan Sudan.
“Babban daraktan NEMA, ya yaba da amincewar da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ba hukumar; domin gudanar da aikin kwaso mutanen.
“Haka zalika, babban daraktan hukumar NEMA ya yaba da irin tallafin da ministar kula da jin kai da agaji da ci gaban al’umma, Hajiya Sadiya Umar Farouq ta bayar.
Ya kuma umarci masu ruwa da tsaki da su ci gaba da hada kai da hukumar NEMA domin tabbatar da cewa an kammala kwaso ‘yan Nijeriya baki daya”.