Tsohon gwamnan Jihar Jigawa, Sule Lamido, ya yi tir da rabon abincin da ɗan shugaban ƙasa, Seyi Tinubu, ya yi a yankin Arewa, yana kallon hakan a matsayin wani raini ga al’adun Arewa. A cikin wani bidiyo da ya yi yawo a shafukan sada zumunta, Lamido ya bayyana hakan a gaban taron mambobin jam’iyyar PDP a lokacin buda baki na Ramadan a garin Bamaina, karamar hukumar Birnin Kudu ta Jihar Jigawa.
Lamido ya ce, “Wannan abin kunya ne ga Arewa da kuma iyayen kasa cewa ɗan Tinubu ya zo Sokoto da Kano ya raba shinkafa da aka dafa. Wannan abu ne mai ɓata sunan mu da al’adu,” in ji Lamido. Ya ƙara da cewa Arewa, wanda aka san ta da kyawawan al’adu da tarihin ta, bai kamata ta koma matsayin neman sadaka ba.
- Malamai Suna Takara Da ’Yan Siyasa Wajen Neman Mulki –Sule Lamido
- El-Rufa’i Ya Yi Kadan Ya Sa Mu Bar Jam’iyyar PDP – Sule Lamido
Lamido ya jaddada cewa mutanen Arewa, wanda suka yi fice a al’adu da tarihi, suna da alhakin kiyaye martabarsu. Ya ambata sunayen jagororin tarihi kamar Aminu Kano, Sardauna, Tafawa Balewa da Joseph Tarka, yana mai cewa, “Dole ne mu tashi tsaye don mu aikata abin da ya dace.”
Rabon abinci da Seyi Tinubu yayi, wanda ya haɗa da rabon kayan abinci a jihohin Arewa daban-daban ciki har da Kano, da Sokoto, da Niger, da Kaduna, Adamawa, Yobe da Bauchi, ya haifar da martani daban-daban. Wasu kungiyoyin Arewa sun yaba da wannan matakin a matsayin taimako ga al’umma masu rauni yayin Ramadan, yayin da wasu kuma suka ke ganin shi a matsayin wata dabara ta siyasa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp