A ranar Lahadi da ta gabata, fusatattun gwamnonin PDP da ake kira da G-5 sun gindaya sababbin sharudda kafin su goyi bayan Atiku Abubakar.
Wannan yana zuwa ne a daidai lokacin da tawagar dan takarar shugaban kasa na APC, Bola Ahmed Tinubu da takwaransa na jam’iyyar LP, Peter Obi suke zawarcin gwamnoni domin su mara musu baya a zaben shugaban kasa na 2023.
- Tsoma Baki Da Lalata Tsarin Samar Da Kayayyaki Da Amurka Ke Yi Bai Samu Karbuwa Ba
- Dalibi Ya Rataye Kansa Har Lahira Saboda Budurwarsa Ta Auri Wani A Gombe
Da suke jawabi jin kadan bayan ganawar sirri a Jihar Legas, gwamnonin sun bayyana cewa har yanzu kofar yin silhu da Atiku a bude take.
A wurin ganawar akwai gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike da gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde da gwamnan Jihar Benuwai, Samuel Ortom da gwamnan Jihar Inugu, Ifeanyi Ugwuanyi da gwamnan Jihar Abiya, Okezie Ikpeazu da tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar PDP, Cif Olabode George da tsofaffin gwamnoni wadanda suka hada da Ayodele Fayose (Ekiti) da Donald Duke (Kuros Riba) da Olusegun Mimiko (Ondo) da kuma Jonah Jang (Filato).
Haka kuma akwai tsohon ministan shari’a, Mohammed Adoke da mataimakin shugaban jam’iyyar PDP na yankin kudu, Taofeek Arapaja da Sanata Nasif Suleiman da Sanata Sandy Onor da kuma Sanato Sam Ohabunwa.
Ganawar ta gudana kwanaki kadan bayan gwamnaoni sun bayyana dan takarar gwamnan Jihar Ribas, Siminalayi Fubara. Sun gudanar da irin wannan ganawa a Inugu da Benuwai da kuma kasashen ketare. Gwamnonin sun yi bore ga Atiku kan kin dakatar da shugaban jam’iyyar PDP, Iyorchia Ayu.
Da yake magana a wurin ganawar, Makinde ya bayyana cewa shi da sauran abokanansa za su ci gaba da fafatuka har sai shugabannin jam’iyya da sauran dattawan jam’iyyar sun dawo daga hayyacinsu.
Ya ce, “Mun hadu ne a wannan wuri domin ganawa da sauran jiga-jigan jam’iyyar PDP. Mu ne gwamnonin guda biyar da ake kira G-5, wanda muka kasance sabuwar tawaga masu mutunci.
“Idan aka kallemu za a ga cewa gwamnoni ne guda biyar da suke ci gaba da fafatuka, kuma mu a yankin kudu maso yamma mun sake bibiyan al’amuran jam’iyyar domin ganin abubuwan da suke gudana game da zabe mai zuwa.”
Bayan ganawar sirrin, Jang ya jaddada cewa suna nan a kan matakansu kan abubuwan da suka tattauna a Fatakwal.
“Bayan nazari kan abubuwan da suke gudana a jam’iyyar, mun cimma matsaya kan yanke hukuncin da muka zantar a garin Fatakwal. Sannan mun gana a nan ne domin jaddada matsayarmu wajen bude kofar tattaunawa da jam’iyyarmu ta PDP,” in ji shi.
Gwamnonin sun gudanar da ganawar ce a dakin taro na George da ke Ikoyi, inda Wike ya bayyana cewa za su goyi bayan jam’iyyarsu a zabe mai zuwa matukar aka biya musu bukatocinsu.