Shugabannin majalisar dattawa sun yi ganawar sirri da hafsoshin tsaro kan matsalar tsaro a kasar nan.
Kamfanin dillancin labarai na Nijeriya (NAN) ya ruwaito cewa, a wajen taron akwai babban hafsan sojin kasa, Janar Lucky Irabor; Shugaban hafsan soji, Laftanar-Janar Faruk Yahaya; Babban Hafsan Sojan Ruwa; Vice Adm. Awwal Gambo, da babban hafsan sojin sama; Air Marshal Oladayo Amao.
Sauran sun hada da Sufeto-Janar na ‘yan sanda, Usman Baba; Babban Darakta Janar na Hukumar Tsaro ta farin kaya (DSS), Yusuf Bichi; Babban kwamandan hukumar tsaron farin kaya ta Nijeriya, Dr Ahmed Audi da babban daraktan hukumar leken asiri ta kasa NIA; Ahmad Abubakar.
NAN ta kuma ruwaito cewa, mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Babagana Monguno, an ce yana halartar taron majalisar zartaswa na tarayya (FEC) na mako-mako lokacin da aka yi zaman sirri a majalisar dattawa, bai sami Halartar zaman majalisar dattawan ba.
Da yake jawabi a wajen bude taron, shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, ya ce kalubalen tsaro ya kice ya ki karewa, ammala majalisa ta na fatan a wannan zama za a lalubo bakin zaren, tana kuma fatan al’amura zasu daidaita.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp