Cikin martani da ta sha samu a shafin ta na Tiwita, Maureen Huebel ta fuskanci tsangwama, inda wasu suka kira ta da “Mutum-mutumi”, kana daga baya aka rufe shafin ta.
Wannan malama ‘yan kasar Australia, ta ce ta fuskanci tsangwama ta yanar gizo, saboda ta bayyana burin ta na neman fahimtar ainihin halin da jihar Xinjiang ta kasar Sin take ciki. Ta ce “Wasu mutanen sun fi son su kirkiri karairayi game da kasar Sin don karkatar da tunanin al’umma, saboda suna tsoron bincike ne zai iya tona asirin labaran karya da suke bazawa game da Xinjiang.
A tsawon lokaci, wasu kafofin watsa labarai na yammacin duniya da ‘yan siyasa, sun rika yayata kalaman batanci irin su zargin “Kisan kiyashi a Xinjiang”, kalaman da Huebel ke kaffa-kaffa da amincewa da su. A cewar ta, “Na san ma’aunin tattalin arzikin Xinjiang, wato GDPn jihar na ta karuwa cikin sauri, kana yawan al’ummar jihar ma na karuwa.
Domin fahimtar ainihin yadda lamarin yake, sai ta bude shafin Tiwita domin gudanar da bincike, wanda cikin sauri ya janyo dubban masu ziyartar sa.
To sai dai kuma, ba da jimawa ba, sai wasu muryoyi suka rika sukar ta, suna kiran ta da “’Yar kanzagin kasar Sin”.
A cewar Huebel, ta bayyana a shafin ta na Tiwita cewa za ta ziyarci Xinjiang a shekarar 2024, domin yin bincike game da shirin rage fatara, wanda hakan ya jawo mata karin hare-hare da zargi iri iri.
Ta rika fuskantar martani irin su “Ke sojar baka ce kawai” da “Ba ki da kunya ko kadan”, amma duk da haka, ta kan mayar da amsa da cewa “Na gode” tare da tambayar masu zargin cewa ana gudanar da kisan kiyashi a Xinjiang, da su kawo shaidun dake tabbatar da hakan.
Kamar kuma yadda kowa ya zata, ba ta samun wata gamsasshiyar amsa. (Mai fassarawa: Saminu Alhassan)