Wani rahoton baya bayan nan da manyan masana da masu ruwa da tsaki a kasar Sin suka fitar, ya fayyace alkiblar da kasar ta sanya gaba, da salon ta na aiwatar da muhimman manufofin gyare-gyare a gida.
Rahoton mai taken “Kara zurfafa cikakkun sauye-sauye domin ingiza zamanantarwa irin ta Sin: Cimma manyan nasarori da gudummawa ga sauran sassan duniya”, ya fayyace matakan Sin na cimma nasarar aiwatar da gyare-gyare a gida daga dukkanin fannoni, da irin tasirin da hakan zai yi ga ci gaban duniya baki daya.
- Shugaban Zanzibar Ta Tanzania: Ba Za Iya Raba Ci Gaban Afirka Da Sin Ba
- Kasar Sin Tana Da Likitocin Kauyuka Miliyan 1.1
Zamanantarwa irin ta kasar Sin manufa ce da za ta haifar da sabon salon ci gaba ga burin dan Adam na samun bunkasuwa da wayewar kai. Musamman duba da cewa tun shekaru da dama da suka gabata, sassan yammacin duniya ke burin cimma nasarar hakan bisa salo na jarin hujja, har ma wasu kasashe na ganin salo daya tilo da zai kai ga samar da nasara ga bil adama shi ne bin matakan wayewar kai irin na yammacin duniya, yayin da jarin hujja ke zama hanya daya tak ta raya tattalin arziki.
To sai dai kuma sabanin hakan, ta hanyar mayar da hankali ga irin kwarewa, da darussa da Sin ta koya a tafarkinta na neman ci gaba, muna iya ganin yadda Sin din ke kara tattara dabaru, da fasahohin zurfafa gyare gyare daga dukkanin fannoni, inda tuni kasar ta cimma nasarar kama hanyar zamanintarwa wadda ta sabawa ta kasashen yammacin duniya kuma mai cike da nasarori.
Manufofin gyare-gyare a gida da bude kofa ga waje na Sin, sun zamo kan gaba a turbar da kasar ke bi ta zamanintar da kai. Kasar Sin na aiki tukuru wajen bunkasa tattalin arziki, wanda hakan ya haifar da bunkasar ma’aunin GDPn ta, har ta kai matsayin ta biyu a duniya ta fuskar karfin tattalin arziki. Cikin shekaru kusan 10, Sin ta yi nasarar tsame mutane kimanin miliyan 100 daga kangin talauci, yayin da adadin Sinawa masu matsakaicin samun kudin shiga ya haura miliyan 400, adadin da ya zamo irinsa na daya a duniya.
A kan wannan sabuwar hanyan neman ci gaba, kasar Sin na nacewa bude kofa domin ingiza nasarar sauye-sauye, da fadada hadin gwiwa tsakanin sassan kasa da kasa, da gina sabbin sassa, domin daga matsayin budadden tattalin arzikinta zuwa matsayin koli, matakin da ko shakka babu zai ci gaba da haifar da gajiya, da alherai masu yawa ga ita kanta Sin din da ma sauran sassan duniya. (Saminu Alhassan)