• English
  • Business News
Wednesday, October 15, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ta Yi Aure Da Cikin Shege, Auren Yana Nan? (Fatawa)

by Dakta Jamil Zarewa
3 years ago
Aure

Malam wata ta yi cikin shege da wani mutum, sai ta nemi wani daban ya rufa mata asiri ya aure ta.

Yanzu sun yi auren, yaya hukuncin auren a Shari’a yake?
Zina sabon Allah ne da kuma yada fasadi a bayan kasa. Aure kuwa sunnar Manzon Allah ne, da samar da zuriya mai albarka.

  • Manomi Zai Iya Sayar Da Hatsinsa Kafin Ya Girbe? (Fatawa)

Kuma an kwadaitar da mu yin sa. Amma Mazhabar Malikiyya suna ganin matar da aka yi zinar da ita sai ta yi jini wanda ake kira Istibra’i, kafin a daura mata aure domin a raba maniyyin zinar da na aure.

Kuma idan har an daura aure ba ta yi wannan jinin ba, to, za a raba wannan auren ko da sun haifi `ya`ya, domin suna ganin an daura auren ne a cikin idda, kuma Allah Ya hana daura aure a cikin idda. Saboda haka, a wurinsu, wannan auren batacce ne kuma rusasshe.

Amma Maz’habar Abu Hanifa da Imam Shafi`i suna ganin macen da ta yi zina, an so ta yi istibra’i kafin ta yi aure, amma idan har an daura auren ba ta yi istibra’i ba, auren yana nan daram, ba za a raba su ba.

LABARAI MASU NASABA

Annabi (SAW) Shi Ne Mai Girman Duk Wani Mai Girma Da Allah Ya Taɓa Yi (2)

Annabi (SAW) Shi Ne Mai Girman Duk Wani Mai Girma Da Allah Ya Taba Yi

Kuma suka kara da cewa ko da tana da cikin zinar ne aka daura mata aure, to, auren yana nan. Sai dai Imam Abu Hanifa ya ce: mijin da ta aura, ba zai sadu da ita ba, har sai bayan ta haihu, ko da kuwa cikin zinar nasa ne ko na waninsa.

Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: “Duk wanda ya yi imani da Allah da ranar lahira, to ka da ya shayar da ruwansa ga shukar waninsa” Abu- dawud : 1847.

Don neman aarin bayani duba : AL-MUDAWWANNAH aL-KUBRAH 2\173 da Al-mugni na Ibnu-Khudaamah 8/79
A fahimtata, fatawar Malikiyya ta fi inganci kafin a yi auren, saboda fita daga sabanin malamai abin so ne, sannan kuma za a kauce wa fadawa hadari, amma idan an riga an yi auren to fatawar Hanafiyya abar lura ce, saboda akwai bambanci tsakanin zina da aure, sai dai ya wajaba şu nisanci saduwa, kafin ta haihu saboda hadisin da ya gabata.
Allah ne mafi sani.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Annabi (SAW) Shi Ne Mai Girman Duk Wani Mai Girma Da Allah Ya Taɓa Yi (2)
Dausayin Musulunci

Annabi (SAW) Shi Ne Mai Girman Duk Wani Mai Girma Da Allah Ya Taɓa Yi (2)

October 10, 2025
Annabi (SAW) Shi Ne Mai Girman Duk Wani Mai Girma Da Allah Ya Taba Yi
Dausayin Musulunci

Annabi (SAW) Shi Ne Mai Girman Duk Wani Mai Girma Da Allah Ya Taba Yi

October 3, 2025
Murnar Maulidin Cikar Manzon Allah (SAW) Shekara 1,500 Da Haihuwa (3)
Dausayin Musulunci

Murnar Maulidin Cikar Manzon Allah (SAW) Shekara 1,500 Da Haihuwa (3)

September 26, 2025
Next Post
Wakilin Sin Ya Bukaci Kwamitin Sulhu Da Ya Soke Takunkuman Da Ya Kakabawa Sudan Ta Kudu

Wakilin Sin Ya Bukaci Kwamitin Sulhu Da Ya Soke Takunkuman Da Ya Kakabawa Sudan Ta Kudu

LABARAI MASU NASABA

Sojoji Sun Fatattaki ‘Yan Ta’adda A Dajin Taraba

Sojoji Sun Fatattaki ‘Yan Ta’adda A Dajin Taraba

October 15, 2025
Xi Jinping Ya Taya Patrick Herminie Murnar Lashe Zaben Shugaban Kasar Seychelles

Xi Jinping Ya Taya Patrick Herminie Murnar Lashe Zaben Shugaban Kasar Seychelles

October 15, 2025
Yajin Aikin: Ɗalibai Sun Bai Wa ASUU Da Gwamnatin Tarayya Wa’adin Kwana 7 Su Warware Rikicinsu

Yajin Aikin: Ɗalibai Sun Bai Wa ASUU Da Gwamnatin Tarayya Wa’adin Kwana 7 Su Warware Rikicinsu

October 15, 2025
Gwamna Diri Da ’Yan Majalisa 23 Na Bayelsa Sun Fice Daga PDP

Gwamna Diri Da ’Yan Majalisa 23 Na Bayelsa Sun Fice Daga PDP

October 15, 2025
Shugaban Kasa Yana Bibiyar Zanga-zangar Matsin Rayuwa – Minista

2027: Babu Ɗan Siyasar Da Zai Iya Ƙalubalantar Tinubu — Fadar Shugaban Ƙasa

October 15, 2025
Tinubu Ya Nemi Jihohi Su Dakatar Da Karbar Haraji A Kan Masu Safarar Kayan Abinci

Haƙar Ma’adinai Ba Bisa Ƙa’ida Ba Barazana Ce Ga Tsaro A Yammacin Afirka – Tinubu

October 15, 2025
Gabar ‘Yan Bindiga A Tsakaninsu Ta Kara Tsanani A Zamfara

‘Yan Bindiga Sun Hana Manoma Girbi A Zamfara, Al’umma Na Neman Taimako

October 15, 2025
‘Yansanda Sun Ceto Mutum 21 Da Aka Sace, Sun Kwato N4.8m Kuɗin Fansa

‘Yansanda Sun Kama Mutum 105, Sun Ƙwato Ƙwayoyi Sama Da 5,000 A Jigawa

October 15, 2025
Sojoji Sun Kama Ƙasurgumin Ɗan Bindiga, Sun Kashe Shugaban IPOB

Sojoji Sun Ceto Mutum 9 Da Aka Sace A Kwara

October 15, 2025
Dalilin Da Ya Sa Mutane Ke Dawowa Jam’iyyar APC — Shettima

Dalilin Da Ya Sa Mutane Ke Dawowa Jam’iyyar APC — Shettima

October 15, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.