Ministan yada labarai da al’adu, Lai Muhammad, ya ce babban kalubalen ta’addanci a Nijeriya ya kare idan aka yi la’akari da matsalar rashin tsaro.
Lai Mohammed ya bayyana haka ne a wani zama na ministoci a taron makon wayar da kan jama’a da kungiyar UNESCO ke shirya wa.
Ya kara da cewa, sojoji da sauran jami’an tsaro sun jajirce wajen kare dukiyoyi da rayukan ‘yan Nijeriya da wadanda ba ‘yan kasa ba.
Ya ce, “Zan iya tabbatar wa, duk sojojinmu da sauran jami’an tsaro suna yin duk mai yiwuwa don tabbatar da tsaro da kare ‘yan Nijeriya da baki da ke zaune a Nijeriya.
“An ragargaji ‘yan ta’addan. An tarwatsa maboyarsu. A yau kasarmu ta fi kowane lokaci zaman lafiya in akayi la’akari da baya-bayan nan, sabida sadaukarwar da jami’an tsaron mu, maza da mata suka yi.
” ‘Yan Nijeriya, farar hula, su ma su ci gaba da lura amma fa firgita ba. Kamar yadda na fada a wata sanarwa ta baya-bayan nan, dangane da matsalar rashin tsaro, mafi munin rashin tsaro a Nijeriya ya kare, ya zama tarihi.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp