ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Saturday, November 15, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Tafiya Da Gwani Mai Dadi

by CMG Hausa
2 years ago
Gwani

Yayin da kasashen Afirka ke kara nuna amincewa da kasar Sin a fannonin hadin gwiwar wanzar da ci gabansu, karin kasashen nahiyar na dada zurfafa hadin gwiwa, da bunkasa ci gaban alakar dake tsakaninsu yadda ya kamata.

Hakan ne ma ya sa a baya bayan nan shugaban kasar Zimbabwe Emmerson Mnangagwa, yayin da yake karbar takardar kama aiki daga sabon jakadan Sin a kasar sa Zhou Ding, ya jaddada burinsa na fadada hadin kai da bangaren kasar Sin a fannoni daban daban.

  • Xi Jinping Ya Nanata Muhimmancin Samun Bunkasuwa Ba Tare Da Gurbata Muhalli Ba

Ga duk mai bibbiyar yanayin alakar dake tsakanin Sin da Zimbabwe, ya kwana da sanin yadda Sin din ta jima tana tallafawa Zimbabwe wajen samar da ababen more rayuwa, ta hanyar samar da kudaden gudanar da manyan ayyukan raya kasa, ciki har da katafaren ginin ofishin majalissar dokokin kasar, da fadada tashar samar da lantarki ta tururi mai zafi, da sake fasali, da kuma fadada babban filin jiragen sama na Robert Mugabe, da zango na uku na aikin samar da hidimar wayar salula ga al’ummar kasar, ayyukan da suka yi matukar taka rawar gani a fannin bunkasa tattalin arziki da zamantakewar al’ummar Zimbabwe.

ADVERTISEMENT

Bahaushe kan ce “Tafiya da gwani mai dadi”. A gani na hakan ne ma ya sanya kasashe masu tasowa ke dada fifita alakar su da Sin, idan ana batun alakar kasa da kasa, kasancewar kasar Sin na nacewa manufar kaucewa tsoma baki cikin harkokin wajen sauran kasashe, da nuna adawa da takunkuman da kasashen yamma ke kakabawa sauran kasashe, ciki har da irin wadanda aka kakabawa kasar ta Zimbabwe.

Baya ga haka, kasar Sin ta yi cudanya, tare da mara baya ga kasashen Afirka, a fannin samar da tallafin yaki da annobar COVID-19 wadda a ’yan shekarun da suka gabata ta addabi duniya baki daya.

LABARAI MASU NASABA

Bangaren Sauka Na Kumbon Shenzhou-21 Ya Iso Doron Duniya

Sin Za Ta Mayar Da Martani Idan Har Japan Ta Aiwatar Da Matakin Da Bai Dace Ba

Hakan ne ma ya sa masharhanta da yawa ke hasashen kara kyautatuwa, da yaukaka, da dorewar alakar Sin da abokan tafiyarta wato kasashe masu tasowa, wadanda suka amince su yi tafiya kafada da kafada da Sin din bisa mutunta juna, da zurfafa musaya a fannonin hadin gwiwa daban daban, karkashin manufofi irin na “Shawarar ziri daya da hanya daya”, da manufar bunkasa ci gaban duniya baki daya.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Bangaren Sauka Na Kumbon Shenzhou-21 Ya Iso Doron Duniya
Daga Birnin Sin

Bangaren Sauka Na Kumbon Shenzhou-21 Ya Iso Doron Duniya

November 14, 2025
Sin Za Ta Mayar Da Martani Idan Har Japan Ta Aiwatar Da Matakin Da Bai Dace Ba
Daga Birnin Sin

Sin Za Ta Mayar Da Martani Idan Har Japan Ta Aiwatar Da Matakin Da Bai Dace Ba

November 14, 2025
Jirgin Ruwan Dakon Jiragen Saman Yaki Na Sichuan Ya Fara Gwajin Sufuri A Karon Farko
Daga Birnin Sin

Jirgin Ruwan Dakon Jiragen Saman Yaki Na Sichuan Ya Fara Gwajin Sufuri A Karon Farko

November 14, 2025
Next Post
Isra’ila Ta Kaddamar Da Manhajar Da Za Ta Samarwa ‘Yan Nijeriya Miliyan Daya Ayyukan Yi

Isra'ila Ta Kaddamar Da Manhajar Da Za Ta Samarwa 'Yan Nijeriya Miliyan Daya Ayyukan Yi

LABARAI MASU NASABA

Masu Kokarin Kashe Kansu Na Kara Karuwa A Nijeriya

Masu Kokarin Kashe Kansu Na Kara Karuwa A Nijeriya

November 15, 2025
Wakilai Daga Jihohi 19 Sun Isa Ibadan Don Taron PDP Na Ƙasa

Wakilai Daga Jihohi 19 Sun Isa Ibadan Don Taron PDP Na Ƙasa

November 15, 2025
Daliban FUTA 240 Sun Samu Digiri Mai Daraja Ta Daya

Daliban FUTA 240 Sun Samu Digiri Mai Daraja Ta Daya

November 15, 2025
Shakirat Ta Tsallaka Mataki Na Ƙarshe Na Zama Gwarzuwar Ƴar Wasan Afrika

Shakirat Ta Tsallaka Mataki Na Ƙarshe Na Zama Gwarzuwar Ƴar Wasan Afrika

November 15, 2025
Wasu Mahara Sun Kashe Mata 2, Tare Da da Ƙona Gidansu A Tudun Yola

Wasu Mahara Sun Kashe Mata 2, Tare Da da Ƙona Gidansu A Tudun Yola

November 15, 2025
Rundunar Sojin Nijeriya Ta Bayyana Dalilan Hana Jami’anta Auren ‘Yan Kasashen Waje

Rundunar Sojin Nijeriya Ta Bayyana Dalilan Hana Jami’anta Auren ‘Yan Kasashen Waje

November 15, 2025
Fashi Da Makami: An Yanke Wa ’Yan Nijeriya Hudu Mazauna Birtaniya Hukuncin Daurin Shekara 55 A Gidan Yari

Fashi Da Makami: An Yanke Wa ’Yan Nijeriya Hudu Mazauna Birtaniya Hukuncin Daurin Shekara 55 A Gidan Yari

November 15, 2025
Shugaban APC Na Kano Ya Nemi Afuwa Daga Al’ummar Fagge Kan Kalamansa

Shugaban APC Na Kano Ya Nemi Afuwa Daga Al’ummar Fagge Kan Kalamansa

November 15, 2025
‘Yansanda Sun Ceto Mutum 21 Da Aka Sace, Sun Kwato N4.8m Kuɗin Fansa

’Yansanda Sun Cafke Wani Da Ake Zargin Dan Ta’adda Ne A Jihar Kebbi

November 15, 2025
Bangaren Sauka Na Kumbon Shenzhou-21 Ya Iso Doron Duniya

Bangaren Sauka Na Kumbon Shenzhou-21 Ya Iso Doron Duniya

November 14, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.