Wasu Jarirai da aka haifa ‘yan uku amma biyu daga ciki suka zo manne da juna, Hassana Isa da Husaina Isa sun tashi daga jihar Kano a ranar Litinin zuwa birnin Riyadh na kasar Saudiyya domin yi musu tiyata a raba su.
Cibiyar Bayar da Agaji ta Sarki Salman (KSARelief) ce za ta gudanar da aikin tiyatar a karkashin jagorancin mai kula da masallatan Harami guda biyu, Sarki Salman bn Abdulaziz.
- Ku Bayar Da Yaranku A Yi Musu Allurar Ragafin HPV Domin Ba Ta Illa Ko Kadan -Mansura Isa
- Majalisar Dokokin Jihar Ribas Ta Fara Shirye-shiryen Tsige Gwamnan Jihar A Yau Litinin
An shirya yin tiyatar ne a birnin sarki Abdulaziz Medical City da ke birnin Riyadh, inda za a yi musu cikakken aikin tantance lafiyarsu karkashin tawagar kwararru da suka hada da likitocin likitancin yara da ma’aikatan jinya da sauransu domin ganin an kammala tiyatar cikin nasara.
Da take zantawa da LEADERSHIP, mahaifiyar tagwayen, Suwaiba Basiru, ta ce ta haifi ‘ya’ya uku, inda biyu daga cikinsu suka zo manne da juna.
Sai dai ta bayyana jin dadin ta da cewa, za a yi musu tiyata domin a raba su ta yadda za su yi rayuwa irin ta duk cikakken dan Adam mai lafiya.