Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, ya bayyana cewa shaidun babbar jam’iyyar adawa ta PDP da ke kalubalantar lashe zabensa ne suka tabbatar masa da nasara cikin rashin sani.
Ya bayyana hakan ne a jawabinsa na karshe ga kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan Kaduna, wanda tawagar lauyoyinsa karkashin jagorancin tsohon babban lauyan gwamnatin tarayya kuma ministan shari’a, Cif Bayo Ojo suka bayyana.
- Hukuncin Kotun Zabe: Martanin Da Atiku Da Obi Suka Mayar Kan Tabbatar Da Nasarar Tinubu
- Kotu Ta Yi Watsi Da Karar Da Jam’iyyar APM Ta Shigar Kan Ingancin Shettima
Babbar Jam’iyyar adawa ta kalubalanci ayyana Uba Sani a matsayin wanda ya lashe zaben da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta gudanar tare da dan takararta Mohammed Ashiru Isa, suna neman a sake sakamakon zabe.
A cikin karar da ake kalubalantar nasarar Uba Sani, masu shigar da kara sun kira shaidu 24 tare da gabatar da su a gaban kotu.
A ranar Litinin 4 ga watan Satumba, kotun sauraron karar zaben gwamnan Jihar Kaduna ta kammala amsar dukkanin shaidun da aka gabatar mata, wanda a yanzu ana jiran yanke hukunci ne kawai.
A cewar gwamnan, masu shigar da kara sun taimaka masa wajen tabbatar da nasararsa ta lashe zaben gwamnan Jihar Kaduna, inda suka yi nuni da karbi shaida daga, Bonett Gwazah, wani babban manazarcin sashen sadarwa a hukumar INEC na Jihar Kaduna.
Gwamnan ta bakin lauyansa ya ce, “Masu shigar da karar sun kira jimillar shaidu 24, wadanda akasarin bayanansu na rantsuwar an gabatar da su ne bisa sammacin da aka bayar a lokacin da ake sauraron karar.
“Bayan an rufe amsar shaidu, wanda ake kara bai da wata bukata ta kira shaidu, bayan da suka fitar da isassun shaidu a karkashin binciken da aka gudanar, wanda shaidun sun goyi bayan bangaren da ake kara”.
Kotun sauraron karar da ke karkashin mai ahari’a, Bictor Obiawie, ta yi alkawarin a kowane lokaci za ta yanke hukunc a nan gaba bisa adalci ga kowani bangare.
Ita ma hukumar zaben wadda ita ce farkon wacce aka shigar da koken a kanta, ta tabo batun wani kuskuren da masu shigar da kara suka yi kan amincewa da takardun zabe.
A halin da ake ciki kuma, dan takarar gwamnan Jihar Kaduna a karkashin jam’iyyar PDP a zaben da ya gudana a ranar 18 ga Maris, 2023, Hon. Isa Ashiru, ya bayyana cewa sakamakon zabe guda biyu masu cin karo da juna da suka fito daga hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) a Jihar Kaduna, wanda a cewarsa, ya hana shi samun nasara a zaben.
Dan takarar gwamnan na PDP ya bayyana haka ne a gaban kotun sauraron karar zaben gwamnan Jihar Kaduna, inda ya kara jaddada cewa INEC ta sauya sakamakon zaben na asali domin bai wa jam’iyyar APC mai mulki a jihar.
Bayan gabatar da jawabinsa na karshe a rubuce a gaban alkalan kotun mai mutum 3 karkashin jagorancin Bictor Obiawie, Ashiru ta bakin babban lauyansa, Oluwole Iyamu ya bayyana cewa INEC ce ta sauya sakamakon zaben.
Ashiru ya kuma yi zargin cewa an samu kuri’u da suka wuce ka’ida da kuma kin bin tsarin zabe, yayin da ya yi kira da INEC kar ta bayyana sunan Uba Sani a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan Jihar Kaduna.
A halin yanzu dai, bayan karbar hujjoji na karshe daga kowani bangare, kotun ta dage yanke hukunci har zuwa wata rana da za ta sanar da lauyoyin nan gaba.
A yanzu haka dai ana dakon yanke hukunci na karshe.