Shirin fim din AKASI shiri ne mai dogon zango, wanda aka fara sakin sa ranar 7 ga Maris, 2024. Da yake an jima ana dakon lokacin sakinsa, Rumbun Nishadi ya ji ta bakin mashiryin fim din YAKUBU PRODUCER GWAMMAJA game da abin da ya kunsa da kuma sauran batutuwa kamar yadda za ku ji a tattaunawarsa da wakiliyarmu, RABI’AT SIDI BALA kamar haka:
abatarwa, ya cikakken sunanka?
Sunana Yakubu Bala wanda aka fi sani da Yakubu Gwammaja.
Me ya ja hankalinka har ka shirya shirin AKASI, kuma a kan me yake magana?
Yawan fyade da ake yi wa kananan yara abin yana min ciwo matuka, da kuma take gaskiya wajan masu wadata.
Shin labarin AKASI gaskiya ne ko kuma kirkirarren labari ne?
Gaskiya labarin Akasi kirkira ne, amma yana faruwa a gaske tunda ai yanzu zalinci ya zama ruwan dare mai kudi ya take talaka duk ba wani sabon abu bane a wannan doron duniya.
Ya batun kudaden da aka kashe wajen gudanar da shirin, kana ganin kwalliya za ta biya kudin sabulu wajen mayar da kudadden da aka kashe ko kuwa?
Gaskiya an kashe kudi har sai da ta-kai-ta-kawo ina jin haushin kashe su tabbas a aljihuna suke fita har ta sa na kasa jituwa da duk wanda zai damu ‘ed producer’ a kan tambayar a karo kudi duba da yadda na ga yana kokari matuka tun daga abinci biyan kowa hakkinsa da mu kanmu manyan ma’aikata babu wanda Baba Hayatu ya tauyewa hakki ma sha Allah. Kuma karshe kwalliya ta biya kudin sabulu manyan gidajen suka rika nemansa domin ganin sun saya sun saka gidajen tb nasu, a karshe aka daidaita da DStb suke haskawa, a YouTube kuma muryar Hausa tb duk Alhamis misalin karfe takwas da rabi na dare.
Ya batun tattara jarumai dan gudanar da shirin, shin ka samu wani kalubale daga wannan bangaren ko wani banfaren daban game da shirun AKASI ko kuwa babu wani kalubale?
A gaskiya tunda nake shirin fim sama da shekara ashirin ban taba fim mai wuyar Akasi ba, idan ka cire wani fim dina mutanen farko, Akasi ya hada jarumai masu yawan gaske jiya da yau, idan ka ce za kai aiki da wanda ya manta aiki tsawan shekara goma baya gwagwarmaya tabbas ba karamin kalubale bane, domin a lokacinsu idan jarumi ya zo ya kan fadi lokacin zuwansa da tafiya, sabanin yanzu ‘series film’ idan ka zo ‘day one’ kawai ka zo ne sai an tashi ka tafi, amma wata wanda na sakaya sunanta babbar jaruma ce ada ta kan ce awa daya na baku idan baku gama ba wallahi tafiya zan yi, aikuwa cikin ikon Allah ba ta karawa mun sami kalubale iri daban-daban, saboda yawan mutanan da aka tara da yawan gidan labarin yayi yawa, har sai da na ce mai ya sa muka sa gidaje haka da yawa.
Ya ka ke kallon karbuwar shirin wajen masu kallo musamman yadda yake sauka a yanzu?
Shirin Akasi ban so ya zo a lokacin Ramadan ba kowa ya san fim idan bai amsa kira ba ya zo a lokacin azumi bai fiya samin magoya baya ba, amma duk da haka Alhamdulilah ana kallo gaskiya, amma na san bayan azumi kowa zai koma daga baya ya gani ya ga mene ne ya faru musamman yadda ya fara daukar dumi yanzu.