An bayyana rashin aikin yi da talauci a matsayin dalilan matsalar rashin tsaro da ya yi wa Arewacin kasar nan katutu.
Bayanin hakan ya fito ne daga bakin shugaban gamayyar kungiyoyin wakilan ‘yan jaridu na Arewa, Kwamared Ibrahim Dan Masani, a jawabin da ya gabatar yayin bude taron shekara- shekara na kwana dada da kungiyar ta yi a Kaduna.
- Wa’adin Da Gwamna Kano Ya Dauka Na Yi Wa Kwamishinoni Hisabi Ya Cika: Kila Wasu Za Su Karbi Littafinsu A Hannun Hagu
- Gwamnatin Tarayya Za Ta Zartar Da Dokar Karya Farashin MagungunaÂ
Dan Masani, ya ce kungiyarsu ta damu matuka da yadda matsalar tsaro ya yi wa Arewa katutu, wanda suke bukatar gwamnati da ta kara zage damtse wajen shawo kan matsalar.
“Matsalar rashin tsaro ba wani abu bane illa rashin abun yi, a kan naira dubu biyu matashi na iya mutum, amma idan gari ya waye matashi ya san inda zai je ya yi aikin da zai samu naira dubu biyar zuwa dubu biyu ba zai shiga damuwar da zai je ya aikata wani abu wanda zai saba tunaninsa ba.”
Taron ya samu halarcin ‘yan kasuwa da jami’an gwamnati da malaman addinin musulunci da kuma masana kan harkokin yada labarai daga jihohin Kano da Kaduna.